Kasar Pakistan ta musanta zargin da Amurka ke yi mata na cewa tana barin 'yan tawaye suna amfani da kasarta wajen kai wa kasar Afghanistan hari.
Babbar Kungiyar bunkasa harakokin ciniki ta kasashen nahiyar Latin Amurka ta Mercosur ta dakatar da wakilcin kasar Venezuela a kungiyar, a sanadin matakin da sabuwar majalisar yi wa kundin tsarin mulki ta Venezuela ta dauka na sallamar babbar lauyar gabatar da shara’oi ta kasar, Luisa Ortega.
Majalisar Dinkin Duniya MDD ta ba da tabbacin samun takardar bayanin Amurka, na ficewa daga yarjajjeniyar Paris Kan Batun Yanayi, "Sai ko idan an sake lale ta yadda sharuddan za su gamsar." a cewar Amurka.
Amurka na kiran da a hanzarta amincewa da daftarin kudurin Majalisar Dinkin Duniya a yau dinnan Asabar, da zai sa Koriya Ta Arewa asarar dala biliyan 1 a shekara guda, daga cikin kudaden shigar da ta ke samu, wadanda da su ta ke gudanar da shirye-shiryenta na nukiliya.
Najeriya ta yi maraba da kudurin gwamnatin Amurka na amincewa sayar mata da jiragen yaki, al’amarin da a baya ya janyo cece-kuce tsakanin kasashen biyu.
A kasar Habasha ko Ethiopia an dage dokar ta-bacin da aka saka tun shekarar da ta gabata, biyo bayan karin samun zaman lafiya.
'Yan Majalisun da aka zaba a kasar Venezuela domin gyara ga kundin tsarin mulkin kasar sun fara aiki, duk kuwa da korafin da ake kan zaben na su.
Yawan yara mata 'yan Najeriya da ake safararsu zuwa kasar Italiya domin yin karuwanci na kara karuwa.
Amurka ta amince zata sayarwa da Najeriya Jiragen yaki na zamani samfurin Super Tucano domin ta yaki ta'addanci.
Amurka ta yi Allah wadai da matakan gwamnatin kama-karyar kasar Venezuela, bayan kame wasu shugabannin hamayyar kasar biyu.
An kafa dokar hana Amurkawa bulaguro zuwa kasar Koriya ta Arewa, domin kare su daga fadawa hannu da dauresu ba tare da sun aikata laifi ba.
Noma Tushen Arziki
Jiragen saman yakin Amurka masu lugudan bama-bamai sunyi shawagi a saman ruwan Koriya, a wani mataki na mayar da martani kan gwajin makami mai linzami da Koriya ta Arewa ta yi.
Jami'an Tsaron Australia sun dakile wani shirin 'yan ta'adda na harbo jiragen sama a kasar.
An kai wani mummunan harin kunar bakin wake a birnin Mogadishu na kasar Somaliya a yau Lahadi.
Gwamnatin jihar Taraba ta kaddamar da aikin hanyar zuwa Pantisawa da aka yi watsi da ita fiye da shekaru goma.
Jirgin ruwan yakin Amurka ya yi harbin gargadi ga jirgin ruwan kasar Iran ta hanyar da bai dace ba.
Amurka ba zata yarda Koriya ta Arewa ta mallaki makamin Nukiliya ba, Kuma tayi kira ga Rasha da China su dauki mataki.
Kungiyar Boko Haram karkashin shugabancin Albarnawi, ta fitar da wani hotan bidiyon wasu ma’aikatan jami’ar Maiduguri guda uku da suka yi garkuwa da su.
Gwamnoni da sarakunan Arewacin Nigeria sun gudanar da taron kwanaki biyu a jihar Kaduna don yin nazari game da irin matsalolin da yankin ke fuskanta.
Domin Kari