Kamfanin dillancin labaran WAM ya fada yau asabar cewa sojojin suna daga cikin wata rundunar da Sa’udiyya take jagoranci, dake yakar ‘yan tawaye ‘yan mazhabin Shi’a a Yemen.
Kamfanin dillancin labaran na WAM yace jirgin ya fadi a lardin Shabwa na kudancin kasar inda jiragen yakin Amurka suke kai farmaki a kan ‘yan kungiyar al-Qa’ida na kasar.
Rundunar da Sa’udiyya take jagoranci tana yakar ‘yan tawayen Houthi masu samun goyon bayan Iran ta sama da kuma ta kasa.
‘Yan tawayen sun kwace birnin Sana’a a shekarar 2015, suka tilastawa gwamnatin da kasashen duniya suka amince da ita ta yi hijira zuwa kasar Sa’udiyya, kafin ta komo birnin Aden mai tashar jiragen ruwa a kasar ta Yemen.
Facebook Forum