Shata kan iyakokin kasashen na zuwa ne sakamakon hukuncin da kotun kasa da kasa ta duniya ta bayar zamanin tsohon shugaba Olusegun Obasanjo domin ya raba gardama kan wasu wurare kamar su Bakassi.
Kakakin gwamnan jihar Adamawa Mr. Yohana Mathias, ya bayyanawa ‘yan jaridu takaicin gwamnatin jihar kan afkuwar lamarin.
Ya kuma musanta rade-radin da ake yayatawa na cewa Boko Haram ce ta kai harin, yana mai tabbatar da ‘yan fashi ne suka farma tawagar.
Wata majiya da ba ta amince a ambaci sunan ta ba ta fadawa Muryar Amurka cewa wasu gungun ‘yan fashi da makami biyu ne suka kaiwa tawagar hari sau biyu a jere bayan sun yi la’akkari da cewa ‘yan sanda biyu ne kacal ke rakiyar tawagar.
SP Othman Abubakar, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda ta jihar Adamawa wanda ya tabbatar da afkuwar lamarin ya ce ba su da masaniyar kan irin kariya da jami’an tsaron Kasar Kamaru suka baiwa tawagar, kasancewar tawagar su ce ta raka ayarin kan iyakarta.
Daga cikin wadanda suka rasa ransu a tawagar Majalisar Dinkin Duniya akwai mutanen kasashen Kenya, Kamaru, jihohin Jigawa da Kano da kuma Mal. Zakari Bakari na ma’aikatar filaye da safiyo ta jihar Adamawa.
Ga Karin bayanin rahoton Sanusi Adamu.