Shugaban kungiyar malamai ta kasa reshen jihar Adamawa Kwamrad Rodney Nathan, ya ce kungiyar ta dauki matsayar kasancewar suna binta albashin watanni hudu, kudin alawus na hutu shekara biyar, rashin karin girma a bakin aiki da kuma rashin kyautata muhallin da dalibai za su rika karbar karatu game da ingantattun kayan koyarwa.
Ya kara da cewa tun da aka ayyana dokar ta bacin sau daya suka zauna da bangaren zartaswa kuma kawo yanzu ba a ce da su ci kanku ba.
Da yake wa wakilin sashen Hausa bayanin matakan da suka dauka wajen aiwatar da dokar ta bacin, gwamnan jhar Adamawa Sanata Mohammadu Umaru Jibirilla, ya ce gwamnati ta dauki makaranta ‘daya daga kowace shiyya don kyautata muhallinsu da kyautata jin dadin malamai ta hanyar samar masu da ingantattun kayan aiki da kuma biyansu hakkokinsu.
Wani shugaban makarantar firamare a karamar hukumar Gombi da ke jihar Adamawa da ya nemi a sakaya sunan sa, ya nuna takaicinsa da irin halin da malaman ke rayuwa a ciki na rashin biyan albashi da ta tilastawa wasun su musamman magidanta shiga sana’o’in kamar su barema, awon hatsi da wasu kananan aikace aikace don neman abin sawa a bakin salati.
Wannan yanayi da malamai ke rayuwa a ciki shi ya sa a bikin ranar ma’aikata ta bana ‘ya’yan kunggiyar malaman suka daga kwalaye dauke da sakoni.
Domin karin bayani ga rahotan Sanusi Adamu.
Facebook Forum