Asusun koyar da harshen Larabci na Najeriya ya yi alwashin amfani da gwanancewa a harshen wajen yaki da akidar ta’addanci a Najeriya da kasashen yankin Sahel.
Tsarin inshorar da a ke kira Takaful ya kara samun tagomashin raba rarar kudi ga wadanda suka shiga tsarin da samun miliyoyin Naira.
Gwamnatin Najeriya ta musanta zargin cewa tana sulhu da ‘yan bindiga a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya, tana mai cewa bambancin siyasa ko sabanin tsakanin wasu mutane bai kamata ya shigo lamuran tsaro ba.
Da yawa daga jami’an gwamnatin Tinubu na daukar daukaka karar zabe da manyan jam’iyyun adawa suka yi bayan hukuncin karar zabe da ya bai wa Tinubu nasara a matsayin aikin baban giwa ne.
Sabuwar gwamnatin jihar Zamfara ta gwamna Dauda Lawal ta ce sam ba za ta bi sawun tsohuwar gwamnatin Bello Matawalle ba wajen yin sulhu da 'yan bindiga.
Babban Ministan Lafiya na Najeriya Dr. Muhammad Ali Pate ya ce akwai likitoci da sauran jami'an lafiya sama da 400,000 a Najeriya amma ba su wadatar ba don haka akwai bukatar kari.
Rasuwar babban malamin addinin musulunci na Ahlussunnah a Najeriya Sheikh Abubakar Giro Argungu ya girgiza jama’a da dama inda shafukan yanar gizo su ka cike da ta’aziyya.
Yau Laraba Kotun sauraron karar zaben Shugaban kasa za ta yanke hukumci bayan kwanaki dari da rantsar da Bola Ahmed Tinubu a matsayin Shugaban kasa.
Gwamnatin Najeriya ta bayyana kwarin guiwar samun nasara a kotun sauraron karar zabe da za ta yanke hukunci a Larabar nan kan karar kin amincewa da sakamakon da ya kawo Ahmed Bola Tinubu karagar mulki.
Kungiyar Fulani makiyaya ta MIYETTI ALLAH KAUTAL HORE ta ce iilmantar da 'ya'yan makiyaya ne kadai hanyar raba su da miyagun iri.
Domin Kari