Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba Za Mu Yi Koyi Da Tsohuwar Gwamnatin Zamfara Wajen Sulhu Da Barayi Ba - Sabuwar Gwamnati


Dauda Lawal, gwamnan jihar Zamfara
Dauda Lawal, gwamnan jihar Zamfara

Sabuwar gwamnatin jihar Zamfara ta gwamna Dauda Lawal ta ce sam ba za ta bi sawun tsohuwar gwamnatin Bello Matawalle ba wajen yin sulhu da 'yan bindiga.

A cewar sabuwar gwamnatin, bin tsarin sulhu da tsohuwar gwamnatin ta yi ya janyo kara tabarbrewar tsaro a jihar.

A taron manema labarai a Abuja, sabuwar gwamnatin ta ce za ta yi garambawul ga dukkan matakan tsaro da tsohuwar gwamnatin ta buge a kan su da ta ce ba su haifar da wani sakamako mai ma'ana ba.

Mannir Mu'azu Haidara shi ne kwamishinan labaru na jihar "sam ba za mu yi sulhu da 'yan ta'adda ba don haka za mu dau 'yan sintiri 300 a kowace karamar hukuma don gamawa da miyagun irin."

MANNIR MU'AZU HAIDARA
MANNIR MU'AZU HAIDARA

A martninsa, kakakin tsohon gwamna Zailani Bappah ya ce ko gobe suka samu dama sai sun dawo da sulhu.

"A duk wata fitina da a ka yi a duniya karshe dole sai an dawo teburin sulhu don samar da maslaha." Ya ce.

Kwamishina Mannir Haidara ya zargi jami'an tsohuwar gwamnatin da yin warwason kayan gwamnati bayan faduwa zabe.

A nan kuma Zailani Bappah ya aza alhakin warwason kan zauna gari banza "An yi dukan mu da kona gidajen mu har sai da 'yan sanda su ka buga bindiga."

Sabuwar gwamnatin ta ce mukamin karamin minista tsaro da a ka ba wa Bello Matawalle bai tsole mata ido ba tana mai cewa tun a kujerar gwamna ma bai tabuka komai ba ta fuskar tsaro.

Saurari rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG