A kaikaice gwamnatin tarayyar Najeriya na magana ne kan tsamar da ke tsakanin tsohuwar gwamnatin jihar Zamfara ta Bello Matawalle da sabuwar gwamnatin gwamna Dauda Lawal Dare, wadanda dabarunsu na yaki da 'yan bindiga suka sha bambam.
Bayan fitowar sanarwar caccaka daga gwamnatin Zamfara, da ke cewa wasu jami'an gwamnatin Najeriya suna shiga wasu yankunan jihar don tattaunawa da 'yan ta'adda ba tare da tuntubar gwamnatin jihar ba, Ministan yada labaran Najeriya Muhammad Idris ya ce sam babu kamshin gaskiya a zargin.
A sanarwar Idris, ya ce maimakon gwamnan Zamfara ya yaba wa gwamnatin tarayya don matakin gaggawa da ta dauka a kokarin ceto daliban jami'ar tarayya ta Gusau da ‘yan bindiga suka sace, sai ya zabi cimma muradun siyasa.
Tun farko dai kwamishinan yada labarai na jihar Zamfara Mannir Haidara, ya bayyana mamaki da takaicin gwamnatin Zamfara kan kutsen jihar da cibiyoyin tarayya suke yi ba tare da tuntubar gwamnatin ba, da sunan sulhu da ‘yan bindiga.
Matakin gwamnatin Zamfara na “ba sani ba sabo” ga 'yan bindiga kusan sauya tsari ne daga abin da tsohuwar gwamnatin Bello Matawalle ta yi, wanda sabuwar gwamnatin ke cewa aikin babban giwa ne.
Koda yake, jami'in yada labaran tsohon gwamnan jihar Zailani Bappah ya ce kamai daren dadewa sai an koma teburin sulhu.
Hakika jihar Zamfara na kan gaba a jihohin arewa maso yamma na Najeriya da suka dandana hare-haren barayin daji. Sai dai duk da kokarin da hukumomi ke yi a bayyane yake akwai sauran rina a kaba.
Saurari rahoton Nasiru Adamu Elhikaya:
Dandalin Mu Tattauna