Gwamnatin Najeriya ta amince da turawa jihohi kudi fiye da Naira Biliyan 522, don tallafawa jihohin su biya bashin da ma’aikata suke binsu na albashi da fansho.
Gwamnatin Najeriya ta musanta rahotanni dake cewa an samu bullar cutar Polio ko kuma a shan-inna a kudu maso kudancin kasar, bayan da aka haifi wani yaro da nakasa a jikinsa.
Umarnin da shugaban Najeriya Mohammadu Buhari ya bawa ministan Shari’a Abubakar Malami, na cewa ya gudanar da bincike kan kowaye aka samu da laifin zarmiya a gwamnatinsa da alwashin gurfanar da duk wanda aka samu da laifi gaban kotu.
Kungiyoyin manoma dake raya kiwo da noma a yankunan karkara sun gudanar da wani taro a birnin Abuja, gabannin babban taron Ministocin aikin gona na kungiyar ECOWAS.
Majalisar Dinkin Duniya ta ware duk ranar bakwai ga watan Disamba don tunawa da kuma bunkasa harkar sufurin jiragen sama na fararen hula.
Babban kotun tarayyar Najeriya ta bayar da hukuncin a saki Mallam Ibrahim El-Zakzaky cikin kwanaki 45, a kuma bashi diyyar Naira Miliyan 50.
Ministan ya rasa ransa ne tare da dansa lokacin da motarsu tayi hadari kan hanyar Abuja zuwa kaduna.
Yayin da akasarin talakawa ba su maida hankali ga abubuwan dake haddasa sauyin yanayi, kwararru su na gargadin cewa idan ba a yi wani abu yanzu da sauri ba, illar da zata yi zai rutsa da dukkan bil Adama.
A zaben bana, jam'iyyun siyasa a Najeriya sun rungumi sabon salon bakanta juna maimakon mayarda hankali kan abubuwan da suka yi ko zasu yi ma jama'a.