Ba bakon abu ba ne sauyin yanayi a lokutan damuna ko rani, hunturu ko lokacin zafi a kasashen yankin Sahel ko kudu da Sahara da ya hada da sassa da dama na arewacin Najeriya musamman jihohin kan iyaka.
Tun kafin mu yi nisa cikin wannan rahoto masanin harkokin muhalli Hussaini Jar Kasa ya ambata tushe da illolin dumama ko sauyin yanayi ga sassan Najeriya. "Iskar nan mai guba akwai Carbon dioxide akwai su Methane akwai su Fluorocarbon. Su wadannan su Fluorocarbon wadannan a na samun su daga su AC su firji da dai sauran su. Za ka ga kuma ya na kawo fari.Wani lokaci a samu ruwan sama wani lokacin babu.Akwai wadansu kasashe zuwa nan gaba kadan ruwa ka iya shafe su.Yanzu ka duba Victoria Island a Lagos kusan ruwa ya mamaye yankin."
Shin wanne canji mutane ke lura da shine ga muhallin su, ko dai ba sa gane ko an samu canji koko a'a? Na shiga cikin birnin Abuja don samo amsa.
"Suna na Amina Aliyu Usman, in ka duba yadda iska ke hurawa musamman da asuba da yadda kura ke tashi a ko ina duk alamu ne na hamada."
"Suna na Musa Bala Yakasai, ni ne 'National Coordinator'na 'Arewa Green Movement' Akwai wani abu da a ke kira a turance 'RIVER BANK' shi Kogin Hadejada Jama'are ya taho ne daga yanki da ya hada da tafkin Chadi. Don haka sai an yashe kogin Hadeja da Jama'are kafin ruwa ya gudana yadda ya dace.Manoma su samu gabban ruwa har waje ya yi tsirrai ya zama kore shar."
"Suna na Aliyu Salihu. Da in ka shigo yanki na arewa za ka ga damshi ko da ruwa ya dauke za ka ga idon ruwa daga kasa har a rika noma dankali da sauran abubawa irin su tumatur. Abun da ya ke kawo wannan duk da ni ba kwarerre ba ne amma in ka duba ayyukan gine-gine da masu shiga daji su saro itace su maida shi gawayi, hakan ya sanya yanayi ya sauya."
Jami'ai a nan Najeriya na ba da tabbacin bi sau da kafa irin shawarwari da kwararru a matakin duniya da majalisar DINKIN duniya ke bayarwa kan yadda za a farfado da lafiyar muhalli.
Shugaban hukumar yaki da hamada ta Najeriya Goni Ahmad na bitar illar da ta ke tinkaro al'ummar arewacin Najeriya matukar ba su dage ga kare muhalli ta hanyar dasa bishiyoyi da kaucewa kona daji ba.
Ya ce, "Hamada fa ba karamin illa ba ne saboda idan hamada ya faru wannan iskan ya zo ya wuce yashin nan ya zo ya bunne waje gaba daya kafin ka sa ke mayar da shi ka koma baya ka ce ka samu amfani a wannan wajen shekaru fa zai jawo. Saboda haka rigakafin da a ke yi yanzu a soma wadannan dashe-dashen a kare wannan zafin. Don wannan zafin yanzu dan kadan ne bai yi zafi sosai ba. Idan ya wuce matsayin da turawa ke kira 'POINT OF NO REVERSAL' ba za ka sake maida shi yadda ya ke ba. Wannan abun mu tsaya mu duba da kadan-kadan ne ya ke shigowa kasarmu. In ka na ganin wanda ya ke Sokoto,ko Wanda ya ke Borno ko ya na Katsina da sauran can baya abun na damun shi kai da ka ke cikin gari ya jawo har ma ya shigo Abuja da kadan-kadan kwararowar nan zai zo. Idan ba mu tsaya mun yi maganin shi tun yanzu zai mamaye kasarmu. Ga shi kuma 'already' mun fara ganin 'climate chnage' ya fara isowa wurin. To amma in akwai dashe-dashe da sauran to Allah zai kawo yanayi ya saukaka wadannan abubawa din iskar ta canza. In zafi a ke yi za ka ga sanyi ya dawo. Kuma har dabbobi ba na gida ba na daji ma za su dawo."
Labarin illar da dumamar yanayi ya ke yiwa malafar nan ta duniya da ke rage zafin rana "Ozone layer" sanenne ga al'umma da ke ganin canjin a zahiri inda dazuka su ka zama birane ko tarin yashi , hakanan gonaki da dama sun rage yawan yabanya don mutuwar sinadaran kasa da ke taimkawa shuka girma.
Shin al'umma za su iya yaki da hamada ko dai za su bari hamadar ta yi galaba kan su cikin yakin da ba ya bukatar masu ko takubba?."