Najeriya ta amince da dawo da hasken wutar lantarki ga jamhuriyar Nijar bayan janye wasu takunkumai da Kungiyar Raya Tattalin Arziki Kasashen Afrika ta Yamma, ECOWAS, ta yi kan kasar.
Yayin da talakan Najeriya ke ci gaba da dandana kudarsa, hankula na dada karkata kan rawar da tashin farashin dala ke takawa.
Shugaban hukumar yaki da cin hanci ta ICPC, Dakta Musa Adamu Aliyu ya ce ba lalle sai an kafa kotuna na musamman ba don sauraron shari'un cin hanci da rashawa.
Tsohon gwamnan jihar Yobe Sanata Bukar Abba Ibrahim ya rasu yana da mai shekaru 75.
Hukumar alhazan Najeriya (NAHCON) ta ayyana farashin kujerar hajjin bana da ya doshi Naira miliyan 5.
Bayan shafe dare da wuni daya su na yajin canjin kudi, 'yan kasuwar canji a Abuja sun tsaida shawarar janye yajin don komawa aiki a yau jumma'a.
A lokaci kadan daga yanzu Kotun Kolin Najeriya, wacce ita ce ta karshe za ta yanke hukuncin zaben gwamnonin jihohin Kano, Zamfara, Nasarawa da Filato.
Shugaban gwamnonin arewacin Najeriya Muhammadu Inuwa Yahaya ya bayyana cewa, an mance da aikin tono danyen man fetur a Arewacin Najeriya bayan kaddamar da rijiyoyin fetur na Kolmani a Gombe da Bauchi.
Akeredolu ya yi fama da cutar daji tsawon watanni wanda hakan ya sanya shi kwantawa a asibitin Jamus inda rai ya yi halinsa a ranar 27 ga watan Disambar 2023.
Hukumar alhazan Najeriya NAHCON ta kara wa'adin lokacin biyan kudin ajiya don samun kujerar aikin Hajjin bana 2024 zuwa karshen watan nan na Janairu.
Kungiyar 'yan boko ta Tijanniyya wato "International Tijjaniyya Burotherhood" ta bukaci 'yan Izala su bar 'ya'yan kungiyar su sakata su wala wajen yin wazifa a masallatan jami'o'i.
"Ba ta yadda gwamnati za ta bari a yi irin wannan laifi ba ta hukunta wanda a ka samu da laifi ba." Ya ce.
Sabon shirin AREWA A YAU zai yi bitar wasu daga darussan da shirin ya tabo a shekarar nan ta 2023 mai bankwana. Daya daga shirye-shiryen shi ne dokar amincewa da kafa hukumar kula da almajirai da tsohuwar gwamnatin shugaba Buhari ta yi ta na jajiberin sauka daga mulki a karshen watan Mayu.
Hankali ya koma kotun kolin Najeriya a jajiberin sauraron daukaka karar gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, kan kalubalantar hukuncin kotun daukaka kara da ya soke zaben sa tare da bai wa abokin hamayyar sa Nasiru Yusuf Gawuna nasara.
Sabon shirin AREWA A YAU zai duba yanda zauren kwararru na arewa da ke bunkasa shiga fasahar ilimin na'urori da duniya ta tinkara 100% sun fara rangadin sassan arewa don wayar da kan matasa wannan hanya.
Domin Kari