A Najeriya bisa ga yadda matsalolin rashin tsaro ke ci gaba da wanzuwa, duk da kokarin da ake yi na magance su, ‘yan kasar sun soma tunanin cewa ya kamata gwamnati ta kirkiro runduna ta musamman daga cikin jama'ar yankunan da ke fama da matsalolin su kare yankunan su.
A Najeriya nasarorin da kungiyoyin fafutukar kare hakkin yara ke samu na haduwa da cikas domin wasu na yi masu zagon kasa, sai dai kuma kungiyoyin da hukumomin kare hakkin bil'adama sun ce sai sun ga abinda zai turewa buzu nadi.
A Najeriya gwamnonin kasar sun sha alwashin jajircewa ta kowace hanya za'a samu saukin matsalolin rashin tsaro, zasu bi ta don ganin an samu shawo kan matsalolin.
A Najeriya bisa ga yadda lamarin tsaro ke ci gaba da tabarbarewa a yankin Arewa da kuma kasawar gwamnatin kasar wajen magance matsalar ya sa gamayyar kungiyoyin Arewa ta dora alhakin faruwar matsalolin kan gwamnatin kasar.
Gwamnatin mai girma Muhammadu Buhari ta kan aika mutane a je a yi wa jama’a jaje a nuna rashin jin dadi kuma a yi musu tabbacin cewa an kawo karshen wannan al’amarin.” In ji Monguno.
A Najeriya yawan hare hare da kissan kiyashi da ake yi wa ‘yan kasar na ci gaba da tunzura jama'a har sun fara tunanin daukarwa kan su mataki sabodagwamnati ta fita batun su.
A Najeriya jama’a na ci gaba da yin tofin Allah tsine akan yadda mahukumta ke zura idanu ana yiwa jama'ar kasar kissan kiyashi, a daidai lokacin da ake ci gaba da alhinin kisan gilla da ‘yan bindiga suka yiwa matafiya da hukuma ta tabbatar da adadinsu ya kai 23.
A Najeriya kungiyoyi da hukumomi da ke fafatukar kare hakkokin bil'adama na ci gaba da daura damarar ceto rayukan jama'a musamman kananan yara da kan iya fadawa tarkon cin zarafi.
A Najeriya jama'ar kasar na ci gaba da shiga halin kunci sanadiyyar ayyukan ‘yan fashin daji wadanda ke hana su yin bacci da ido biyu rufe.
A Najeriya mahukunta na kan daukar matakan shawo kan matsalolin rashin tsaro da suka ki ci suka ki cinyewa wadanda ke ci gaba da addabar jama'ar kasar.
Yayin da masu lalura ta musamman a fadin duniya ke amfani da wannan rana da Majalisar Dinkin Duniya ta ware masu, a Najeriya masu lalura sun koka ne kan watsi da su da su ka ce an yi.
A Najeriya karancin samun wutar lantarki na tilasta wasu asibitoci na Jihohin da ke makwabtaka da Jamhuriyar Nijar tura gawarwakin zuwa kasar domin kar su lalace saboda rashin sanyi a wuraren ajiye su.
A Najeriya fafatukar da hukumomi da kungiyoyi ke yi na kare hakkokin kananan yara na kara habaka domin an soma samarda dokokin da zasu kare hakkin yaran da ma basu zo duniya ba.
Likitocin da ke tiyatar zuciya a Najeriya sun fara daukar matakin shawo kan karamcin cibiyoyin tiyatar zuciyaa kasar.
Kungiyar hadin kan 'yan arewa da ake kira Zumunta a Amurka ta tallafa wa al'ummomi da ibtila'in tashe-tashen hankula suka daidaita a jihar Sokoto.
A Najeriya daidai lokacin da wasu al'ummomi ke dakon a bude kasuwanni bayan ‘yan fashin daji sun nada musu hakimai, masana harkar tsaro sun ce wannan abin yana da hadarin gaske ga kasar.
A Najeriya wasu al'ummomi na nuna damuwa akan yadda gwamnatin kasar ta nuna tana iya samar da tsaro ga harkar siyasa, amma ta kasa samar da wadataccen tsaro ga yankunan da ke fama da matsalolin ‘yan fashin daji, aka kuma bar su suna yadda suke so.
A Najeriya bayanai na nuna cewa bijerewa ga umurnin jagoranci da wasu fulani suka yi fiye da shekaru dari biyu da suka gabata shine ya haifar da zaman su cikin jeji har suka nisanta da jama'a.
A cewar masanan, muddin ba a sauya salon yadda ake tafiyar da shari'ar wadanda ake zargi da laifukan ba, hakan zai yi ta mayar da hannun agogo baya.
Fulani da ke jihar Zamfara sun nemi hukumomi su kare rayuka da kaddarorinsu daga 'yan sa kai da ke kaiwa wadanda ba su ji ba, ba su gani ba hari da Fulani ke gani a matsayin daukar fansa.
Domin Kari