Dandalin gwamnonin Najeriya a karkashin shugabancin gwamnan jihar Ekiti Kayode Fayemi sun kai ziyara a jihar Sokoto, domin jajantawa gwamnati da al'ummar jihar, kan hare-haren ta'addanci da suka yi sanadiyyar rasa gwamman rayuka a 'yan kwanan nan.
Wannan na zuwa ne bayan ziyarar ayarin da shugaban Najeriya ya aika don yin ta'aziya kan matafiya da aka kona, da kuma ganawar da gwamnan jihar Sokoton ya yi da shugaban kasa, inda yayi masa bayani kan yanayin da ake ciki.
Gwamnonin dai sun sha alwashin jajircewa wajen ganin an samu mafita ga wadannan matsalolin na tsaro da ke ci gaba da addabar al'umma a kusan dukkan sassan kasar.
“Kasar mu na bukatar mu jajirce kan gano dalilan wadannan ayukkan na ta'addanci, da kuma mi ke kawo ayukkan ta’addancin?" In ji gwamna Fayemi.
Ya kara da cewa "dole mu zamo cikin shiri a zaman mu na shugabanni mu yi duk abinda za mu iya yi cikin karfin ikon da doka ta ba mu, mu goyi bayan shugaban kasa a kawo karshen wadannan matsalolin, kuma zaman mu gwamnoni za mu ci gaba da yin aiki wajen neman hanyoyin wanzar da zaman lafiya cikin jama'ar mu, da kuma tabbatar da hukumta masu aikata ta'addancin”
Gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal yace lallai akwai bukatar a tashi tsaye ga wannan matsalar, yana mai cewa “ga dukan abubuwan da masu ayukan ta'addanci ke aiwatarwa, a bayyane yake cewa basu da wata kyakkyawar akida kawai su makiyan bil'adama ne kuma mu da muke mutanen kirki, dole mu kalle su a haka kuma mu sa kafar wando daya da su.”
To sai dai sa'o'i kadan kafin zuwan ayarin gwamnonin an samu kai wani hari a yankin na karamar hukumar mulkin Isa a jihar ta Sokoto, har ma muryar Amurka ta zanta da wani wanda ya tsallake rijiya da baya wanda ke kwance asibitin Isa akan raunin da ya samu.
Mazauna yankunan dai na ci gaba da kira ga hukumomi da su kawo musu dauki.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: