Masu ruwa da tsaki kan harkar iliimi a Najeriya na fargaban yanayin da ilimi matakin farko ka iya shiga muddin bai samun kulawa yadda ya kamata.
A Najeriya, ganin yadda har yanzu jama'a ke fama da matsalolin rashin tsaro, ya sa wasu daga cikin jagororin al'ummomi ke dora alhakin cin zarafin da ake yi wa jama'a ga Shugabanni dake rike da madafun iko.
Ayyukkan ta'addanci na ci gaba da ta'azzara a Najeriya a inda ake ci gaba da samun salwanta rayuka da dukiyoyin jama'a.
A Najeriya ayukkan ‘yan bindiga na ci gaba da fadada sannu a hankali zuwa sassa daban daban.
A Najeriya al'ummomi na kara shiga damuwa sanadiyyar ayyukan ‘yan bindiga wadanda ke hana su bacci da ido biyu rufe, abin da wasu jagororin al'umma ke ganin ya dace mutane su tashi su kare kansu.
A Najeriya ‘yan bindiga na ci gaba da baje hajar su a wasu yankunan kasar tare da kara jefa tsoro cikin zukatan jama'a.
Ministan kwadago Dokta Chris Ngige ya furta wasu kalamai da wasu ‘ya'yan kungiyar malaman jami'o'in ke fargabar suna iya mayar da hannun agogo baya ga kokarin sansantawa tsakaninsu da gwamnati.
A Najeriya fargabar jama'a kan hare haren ta'addanci na kara fadada daga yankunan karkara zuwa manyan birane, abinda masana ke cewa alama ce mai nuna matakan da mahukunta ke dauka basu iya magance matsalolin tsaro, ko a daren Asabar 'yan bindiga sun kai hari a unguwar Gagi da ke Sokoto.
A Najeriya alamu na dada nuna cewa tunkahon da gwamnatin kasar ke yi na bunkasa ciyar da kasa da abinci na dab da tashi tutar babu, saboda yadda ‘yan bindiga suke hana ayi noma a yankunan kasar.
Harin ta'addanci da aka kaiwa ayarin shugaban Najeriya na ci gaba da daukar hankalin ‘yan Najeriya musamman mazauna yankunan da rashin tsaro ya daidaita har wasu na ganin akwai ishara a ciki.
Duk da yake da yawa daga cikin gwamnatoci musamman na arewa sun yi kwaskwarima tare da saka hannu ga dokokin kare ‘yancin kananan yara, har yanzu ana samun mutanen da ke yi wa dokokin karan-tsaye suna cin zarafin yara.
Gabanin tsayuwar arfa ranar jumma'ar nan mai zuwa hukumar alhazan Najeriya NAHCON ta ce alhazai dubu 25 cikin dubu 43 sun isa Saudiyya.
Jam'iyar APC mai mulki a Najeyatana ci gaba da fuskantar barazanar ficewar ‘ya'yanta zuwa wasu jam'iyu, daidai lokacin da jam'iyun ke faman samun jama'a don cin zabubukan shekara ta 2023.
Kasancewar Najeriya daya daga cikin kasashen duniya da suka sanya hannu ga dokar hana fatauci ko hallaka dabbobi masu fuskantar barazanar karewa a duniya, bai sa an daina hallaka irin wadannan dabbobin ba a cikin kasar.
An tabbatar da mutuwar jami'an ‘yan sandan mopol shida, a wani kwanton bauna da ‘yan bindiga suka yi musu a jihar Sokoto.
Wadansu maniyata daga jihar Sakkwato dake arewa maso yammacin Najeriya sun hadu da tsautsayi akan hanyar su daga Isa zuwa Sakkwato inda zasu jirgi zuwa saudi Arabia.
Cibiyar fafatukar wanzar da zaman lafiya ta kasar Amurka ta himmantu wajen karfafa gwiwar wanzar da zaman lafiya a Najeriya yayinda matsalolin rashin tsaro ke ci gaba da haddabar jama'ar kasar.
Yau aka cika shekara daya cif da sace daliban makarantar sakandaren Birnin Yauri dake jihar Kebbi inda har yanzu maharan ke rike da dalibai goma sha daya mata.
Wadansu ‘yan gudun hijira a Najeriya sun yi dace ta wajen samun tallafin gidaje kyauta daga al'ummomin kasar Qatar a daidai lokacin da dubban ‘yan gudun hijira ke zama a matsugunan wucin gadi marasa inganci.
A Najeriya masana lamurran tsaro na ganin rashin daukar shawarwari da ake bayarwa ga gwamnati ba daga cikin abubuwan da suka sa aka kasa kawo karshen matsalolin rashin tsaro dake addabar kasar.
Domin Kari