Wadannan alhazan sun hada da na jihohi dubu 33 da na jirgin yawo dubu 9 da 'yan kai.
NAHCON da ke amfani da kamfanonin jirage 3 biyu na gida daya na Saudiyya na nuna kwarin guiwar kammala jigilar gabanin rufewar karshe ranar laraba.
Tun a lahadin nan a ka rufe damar shigar jiragen alhazai Saudiyya in ka debe FLYNAS na Saudiyya da kuma kamfanin MAX da ya damu izinin cigaba da jigilar.
Jagoran kamfanin FLYNAS a Najeriya Umar Kaila ya ce za su yi duk abu mai yiwuwa wajen tabbatar dukkan alhazai sun samu sauke faralin a bana bayan dakatar da damar tsawon shekaru biyu a sanadiyyar cutar annoba.
Kaila ya nuna takaicin yanda jinkirin da a ka samu daga jigilar alhazan Abuja ya jawo tsaiko da kuma asarar kimanin dala miliyan daya ga kamfanin.
Jami'ar labarun alhazan Fatima Sanda Usara ta ce akwai tsarin da a ka yi bana don walwalar alhazan da kuma cigaba da samar da abinci irin na Najeriya.
A gaskiya bana da yawa masu niyyar zuwa hajjin sun kwance damara don rashin samun VISA da kuma karancin kujerun da a ka samu da su ka gaza bukatun jama'a.
Akwai mamaki yanda mutane su ka nace da zuwa hajjin bana duk da tsadar da kujerar ta yi mafi tsanani a tarihi da hakan ke nuna marmarin musulmi kan wannan babbar ibada.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: