SOKOTO, NIGERIA - Abinda ke nuna hakan shi ne yadda manoma ke kokawa kan barazanar da su ke fuskanta duk da matakan da mahukunta ke dauka.
Gwamnatin Najeriya mai mulki yanzu tun shekarar 2015 take ikirarin taimaka wa ayyukan noma da karfafa manoma domin wadata kasa da abinci, har ta kai ga nuna dalar shinkafa a jihar Kebbi da babban birnin tarayya Abuja duk da yake dai har yanzu da tsada talaka ke sayen abincin.
Wannan yanayin da aka samar da abincin yanzu ya fara gagarar wadanda ke noman abincin musamman wadanda ke zaune a yankunan karkara a arewacin kasar, saboda ‘yan bindiga suna hana shiga gonaki a yi noman.
Jihar Sakkwato da ke arewa maso yammacin kasar na daya daga cikin jihohin da manoman su ke fama da wannan matsalar, kamar yadda tsohon shugaban karamar hukumar sabon birni, Abdullahi Muhammad Tsamaye, ya Shaida mana.
Yankin Goronyo, duk a gabascin Sakkwato, matsalar daya ce acewar sarkin noman Goronyo, duk da yake ya ce gwamnati na bakin kokarinta. A yankin Isa ma haka abin yake acewar wani mutumin yankin.
A makon da ya gabata rundunar 'yan sanda, ta bakin kakakinta, ta tabbatar wa jaridar Vanguard cewa ‘yan bindiga sun afka gona sun hallaka manoma hudu tare da dauke yarinya ‘yar shekara 18 a wani kauye da ke kusa da Ghandi a karamar hukumar Rabah, sai dai mun yi kokarin kiran kakakin rundunar amma bai amsa kiran ba.
Manoma da ma dukan ‘yan kasa na ganin muddin gwamnati bata dauki matakan gaggawa na manoma su iya yin noman ba, to akwai yuwuwar fuskantar matsalar karancin abinci nan gaba.
Saurari cikakken rahoton daga Muhammad Nasir: