A Najeriya yayin da jam'iyyun siyasa suka ja daga da hanyar tsayar da ‘yan takara domin fafatawa a zabubukan shekara ta 2023, babbar jam'iyar adawa ta PDP na ci gaba da kara samun karfi a wasu Jihohin kasar.
A Najeriya daidai lokacin da jama'a ke ci gaba da alhinin kisan gilla da aka yiwa masu ibadah a jihar Ondo, muhimman mutane na ci gaba da yin Allah wadai da wannan kisan, da kuma kira ga Kirista a kan kar su dau doka da hannu.
A Najeriya masana na ganin sakaci da rikon sakainar kashi ga gwamnati ke yi wa bangaren ilimi shi ke sa ‘yan kasar fita kasashen waje neman ilimi. Wannan na zuwa ne a lokacin da ake ce-ce-ku-ce tsakanin gwamnatin jihar Sokoto da wani dalibi dan asalin jihar mai karatu a kasar Rasha.
A Najeriya korafe-korafe bayan zabuka abu ne da ya zamo ruwan dare, kuma yake ci gaba da wanzuwa duk da illolin da hakan ke haifarwa ga jam'iyun siyasa da ma tsarin dimokradiyya.
A Najeriya alamu na nuna irin rashin tabbas da ake samu tsakanin ‘yan siyasa duk da kokarin da ake yi na sasanta bangarori da ke rikicin cikin gida a jam'iyyun.
A jihar Sakkwato da ke arewa maso yammacin Najeriya jam'iyyar ta gudanar da zaben tsayar da dan takarar ta ta hanyar sasanci wanda gwamna Tambuwal ya jagoranta.
Jagororin al'umma a Najeriya sun yi ittifaki cewa, akwai bukatar karfafa hadin kan ‘yan kasa domin shawo kan yadda kiyayya da juna ke ci gaba da habaka da kuma wanzar da zaman lafiya.
A Najeriya al'ummomi dake zaune akan iyakokin kasar sun jaddada kira akan karin jami’an tsaro a yankunan don taimakawa ga dakile ayukkan 'yan bindiga wadanda ke haddabar yankunan.
A Najeriya wata kotun majistire dake, Sakkwato ta tura mutanen nan biyu da aka kama da ake tuhuma dangane da kisan daliba Deborah Samuel a gidan gyarar hali.
Dilalan man fetur a Najeriya sun yi barazanar daukar kowane irin mataki na ‘yanto kansu daga tanarkin da suka ce gwamnati ta saka su wanda kan yi illa ga sana'ar su.
Bayan wata tarzoma da aka yi yau a Sakkwato, wadda ke da nasaba da zargin sabo da aka yi ma wata dalibar Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari, gwamtain jihar ta kafa dokar hana fita ta tsawon sa'o'i 24 a cikin birnin.
Tuni dai hukumomin jihar Sokoto suka ba da umarnin a rufe makarantar tare da jibge jami'an tsaro don kare rayuka da dukiyoyi.
A Najeriya, matsalolin rashin tsaro na ci gaba da hana jama'a barci da ido biyu rufe; wasu saboda fargabar abin da ka iya faruwa cikin dare, wasu kuwa don tsaron rayuka da dukiyoyinsu da na al’umma.
Dan majalisar dokokin jihar Sokoto mai wakiltar yankin Bello Isa Ambarura ya tabbatar da aukwar harin.
Babban Hafsan sojin Najeriya Lt Gen Faruk Yahaya ya aza tubalin ginin sabon sansanin soji a yankin Isa dake gabashin Sakkwato arewa maso yammacin Najeriya da ya jima yana fama da matsalolin rashin tsaro.
A Najeriya yadda ‘yan siyasa ke canjin sheka tsakanin jam'iyun kasar na son zama tamkar wani sabon salon siyasar kasar, duk da illolin da ke tartare da yin hakan ga tsarin dimokradiya.
A Najeriya masu aikata munanan ayukka na ci gaba da tafka ta'asarsu watakila saboda ko an kama su ba'a hukumta su yadda zai zama darasi ga sauran jama'a.
A Najeriya lokuta masu daraja ga manyan addinai biyu na kasar na karkata tunanin jama'a ga kyautata cudanya tsakanin juna don nema wa kasar zaman lafiya mai dorewa.
A Najeriya har yanzu dai ‘yan kasar na ci gaba da fuskantar matsalolin da ka iya zama sanadiyar salwantar gomman rayukan jama'a a sassan kasar daban daban.
A Najeriya alamu na dada tabbatar da rahotannin da hukumar kididdiga ta kasar ke fitarwa a kan Jihohin da ke da matsanancin talauci musamman ma dai na yankin arewacin kasar.
Domin Kari