Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZAUREN VOA: Tattaunawa Ta Musamman Da Gwamnonin Jihohin Jigawa, Neja Da Maitaimakin Gwamnan Jihar Sokoto - Yuni 08, 2024


Medina Dauda
Medina Dauda

Shirin Zauren VOA na wannan makon zai kawo muku tattaunawa da wasu daga cikin Gwamnoni Jihohin Arewa Maso Yamma da suka kai ziyara Ofishin Sashin Hausa na Muryar Amurka a Washington DC. Wadanda suka hada da Gwamnan Jihar Jigawa Umar Namadi, Gwamnan Jihar Neja Umar Bago da mataimakin Gwamnan Jihar Sokoto Injiniya Idris Gobir.

Gwamnonin na daga cikin tawagar gwamnoni goma da Cibiyar Koyar da Dabarun Zaman Lafiya ta Amurka (USIP) ta gayyata Washington a kwanan nan.

A yayin ziyarar da suka kai sashen Hausa na Muryar Amurka a Washington DC, gwamnonin sun tattauna kan batutuwa da suka shafi matsalolin tsaro da wasu abubuwa masu muhimmanci a Jihohin su.

Saurari shirin cikin sauti:

ZAUREN VOA: Tattaunawa Ta Musamman Da Gwamnonin Jihohin Jigawa, Neja Da Maitaimakin Gwamnan Jihar Sokoto - Yuni 08, 2024
please wait

No media source currently available

0:00 0:10:10 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG