Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZAUREN VOA: Ci Gaban Tattaunawa Ta Musamman Da Gwamnonin Jihohin Jigawa, Neja Da Maitaimakin Gwamnan Jihar Sokoto - Yuni 15, 2024


Medina Dauda
Medina Dauda

Shirin Zauren VOA na wannan makon zai kawo muku ci gaban da tattaunawa da wasu daga cikin Gwamnoni Jihohin Arewa Maso Yamma da suka kai ziyara Ofishin Sashin Hausa na Muryar Amurka a Washington DC. Wadanda suka hada da Gwamnan Jihar Jigawa Umar Namadi, Gwamnan Jihar Neja Umar Bago da mataimakin Gwamnan Jihar Sokoto Injiniya Idris Gobir.

Gwamnonin na daga cikin tawagar gwamnoni goma da Cibiyar Koyar da Dabarun Zaman Lafiya ta Amurka (USIP) ta gayyata Washington a kwanan nan.

A yayin ziyarar da suka kai sashen Hausa na Muryar Amurka a Washington DC, gwamnonin sun amsa tambayoyi kan matakan da suke dauka kan matsalolin harkokin tsaro a shiyar su, tare da irin shawarwarin da suke ba wa Nuhu Ribado mai ba wa Shugaban Najeriya shawara kan sha'anin tsaro.

Saurari shirin cikin sauti:

ZAUREN VOA: Ci Gaban Tattaunawa Ta Musamman Da Gwamnonin Jihohin Jigawa, Neja Da Maitaimakin Gwamnan Jihar Sokoto - Yuni 15, 2024
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:58 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG