Gwamnatin tarayyar Najeriya ta maida martani kan zargin da gwamnan jihar Kaduna Nasiru El-rufa'i ya yi na cewa wadansu hadiman gwamnati a fadar shugaban kasa suna yi wa jam'iyyar zagon kasa don hana ta samun nasara a zaben da ke tafe.
Rahoton da babban bankin Najeriya ya fitar a shafinsa na yanar gizo ya ce bankin ya kashe dalar Amurka biliyan 11.42 a cikin watanni 7, daga watan Janairu zuwa watan Yuli na shekarar 2022 domin a farfado da darajar naira.
Rundunar ‘yan sandan farin kaya ta Najeriya na binciken gwamnan babban bankin Najeriya Godwin Emefiele bisa zargin aikata laifukan da suka shafi kudi, da tallafa wa ayyukan ta’addanci, da kuma yin almundahana.
Wata kotun tarayya da ke West Virginia a Amurka ta samu wani dan Najeriya mai suna Ayodele Arasokun da laifin damfarar gwamnatin Amurka dala miliyan 60 ta hanyar shigar da bayanan haraji na karya.
Mataimakin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labor Datti Baba Ahmed ya bayyana goyon bayansa kan bukatun malaman makarantar jami’a da ke yajin aiki a Najeriya sama da wata shida kenan.
A kokarinta na neman bada gudummuwa a fannin magance matsaloli masu nasaba da tsaro da tattalin arziki a kasar Ghana, kungiyar tarayyar Turai ta EU ta bai wa wasu kungiyoyin fafutukar raya ci gaban Ghana kimanin dubu dari hudu na Euro don samar da dabarun karfafa tsaron iyakokin Ghana.
Akalla mutane 50 ake kyautata zato suka rasa rayukansu sakamakon harin na ranar Lahadi, ciki har da yara kanana.
Ranar Lahadi gwamnatin kasar Mali ta fadi cewa zata fice daga rundunar dakarun kasashen yammacin Afirka da ke yaki da ‘yan ta’adda don nuna rashin jin dadinta da kin amincewa da ita a matsayin shugabar kungiyar ta G5-Sahel ta yankin, wacce ta hada da Mauritania, Chadi, Burkina da Nijar.
Tsohon zakaran damben boksin na duniya, Floyd Mayweather ya isa Najeriya a ziyararsa ta farko a nahiyar Afirka don tallata wasan gabanin wani wasa da zai yi a Dubai ranar Asabar 14 ga watan Mayu.
Kungiyar Malaman Jami’o’in Najeriya ta ASUU ta tsawaita yajin aikin da ta fara watanni 3 da suka gabata zuwa watan Agusta, bisa dalilai masu alaka da halin ko-in-kula da ta ce gwamnatin Najeriya na nunawa.
Wani bene mai hawa uku, wanda iyalai ke ciki, ya rushe a babban birnin hada hadar kasuwancin Najeriya na Legas, inda mutane 8 suka mutu wasu su 23 kuma suka jikkata, wadanda aka kai su asibiti, a cewar hukumar kai daukin gaggawa a yau Litinin.
Hukumar ta dauki wannan matakin ne bayan wani hargitsi da aka samu a lokacin da Najeriya ta kara da Ghana a wasan neman shiga gasar kwallon ƙafa ta duniya a watan Maris.
A Najeriya, kwararru a fannin shari'a sun mayar da martani akan matakin da Majalisar Dattawa ta dauka na amincewa da kafa karin cibiyoyin horrar da lauyoyi 6 a kasar. A yayin da wasu ke yabawa da yin haka, wasu na cewa siyasa ce kawai.
Wata sanarwa daga rundunar sojan Najeriya ta ce ta kai farmaki a wasu wuraren mayakan Boko Haram a jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya, ciki har da wata kasuwar mayakan.
Najeriya ta shiga jerin kasashe 12 a fadin duniya da aka samu bulluwar sabon nau’in cutar coronavirus da ake kira Omicron. Nau’in cutar da aka gano a kudancin nahiyar Afrika ya shigo Najeriya ne ta hanyar wasu matafiya biyu da suka zo kasar daga Afrika ta kudu.
Wanda ya kirkiro kamfanin Tuwita (Twitter), Jack Dorsey ya ce ya ajiye mukaminsa na shugaban kamfanin sada zumuncin Twitter.
Konturolan gidan yarin jIhar Filato, Samuel Aguda yace fursunoni bakwai ne aka kashe a lokacin da ‘yan bindiga suka kai hari a gidan yarin a jiya Lahadi.
A yayin da a yau Litinin wa’adin da hukumomi suka dibar wa likitoci da daliban makarantun likitanci ke cika domin yin alllurar rigakafin cutar corona, kungiyar kananan likitoci ta SUSAS da kungiyar daliban dake karantar fannin lafiya a jami’ar AbdoulMoumouni sun yi watsi da wannan mataki.
Duk da kokarin da hukumomi a Najeriya da Amurka ke yi na kame da kuma dakile ayyukan 'yan danfarar kudin Banki da aka fi sani da 419 ko yahoo Yahoo a Najeriya, har yanzu wasu 'yan Najeriya, musanman matasa, na ci gaba da gudanar da wannan muguwar sana'ar ta hanyoyi da dama.
Wasu Masana harkokin tsaro sun jingina adadi mafi rinjaye da aka samu na hare-haren 'yan bindiga a jihar Kaduna da irin matsayin da gwamnatin jihar ke kai na cewa babu sulhu tsakanin gwamnati da 'yan bindiga.
Domin Kari