Ziyarar Firai Ministar Denmark Mette Frederiksen ita ce ta farko a Ghana. Wannan ziyarar ta karrama cika shekaru sittin da huldar diflomasiya tsakanin Denmark da Ghana ce. ‘Yan kasar Denmark na ganin kasar Ghana a matsayin muhimmiyar kawar kawance a Afrika ta yamma da baki dayan Afrika.
Hukumomin jamhuriyar Nijer sun bayyana shirin cimma yarjejeniyar odar jiragen yaki da motoci masu sulke daga kasar Turkiya da nufin karfafa wa dakarun kasar gwiwa a yakin da suke kafsawa da ‘yan ta’adda.
A cikin shirin wannan makon a birnin Jos dake arewacin Najeriya, za ku ga yadda kasuwa ta budewa wasu matasa masu kirkire-kirkire da suke sarrafa itace wajen yin cokula da sauran abubuwan kicin, da wasu rahotanni.
A cikin shirin na wannan makon mazuna birnin Jos a arewacin Najeriya su na ci gaba da fama da matsalar karancin ruwa, lamarin da ke sa wasu masu sana’o’i amfani da ruwa mara tsafta wajen wanke-wanke da sauran al’amura, da wasu rahotanni.
A cikin shirin na wannan makon, kungiyar likitoci ta Médecins Sans Frontières ta yi kiran daukan matakin gaggawa don shawo kan barkewar cutar kyanda a jihar Bornon Najeriya, da wasu rahotanni.
A cikin shirin wannan makon hukumomin Najeriya na kara kokari wajen yi wa mutane da yawa rigakafin COVID-19 bayan da aka sami tsaiko wajen yin rigakafin saboda wasu bayanan karya, da wasu sauran rahotanni.
A cikin shirin na wannan makon hukumomin lafiya a jamhuriyar Nijar sun fara aikin rigakafin cutar Coronavirus, bayan China ta taimaka ma kasar da magungunan rigakafin, da wasu sauran rahotanni.
A cikin shirin na wannan makon wasu mata matasa a jihar Sokoton Najeriya su na jan hankalin jama’a bayan da suka rungumi sana’ar gyaran mota, wacce aka san maza ne da ita a wannan yanki na kasar, da wasu sauran rahotanni.
‘Yan bindiga sun yi barin wuta a garin Tunga da ke karamar hukumar Illela a jihar Sokoto, lamarin da ya sa mazauna garin gudun tsira da rayukansu zuwa makwabtan garuruwa.
Tashoshin dakatar manyan motoci sun fara aiki don rage yawan hatsari da ke faruwa a sanadiyyar gajiya da direbobi ke samu a Najeriya.
Karin gidajen adana kayan tarihi a fadin kasashen Turai sun fara duba hanyar maida kayayyakin tarihin da suka kwaso daga wasu wurare.
Sannan a Jamhuriyar Nijar, an soma ayyukan kamun kifi a tafkunan kasar, inda hukumomi kan je domin kaddamar da hakan bayan tsawon lokaci da dakatar ayyukan saboda annobar Coronavirus, da wasu karin rahotanni.
'Yan Nigeria musamman masana tattalin arziki sun fara cece-ku-ce akan kwangilar gyara matatar man fetur da ke birnin Fatakwal da majalisar zartarwa ta Nigeria ta ware zunzurutun ku’di har Naira miliyan dubu 570 domin a yi.
A cikin shirin na wannan makon alkaluman MDD sun nuna cewa kasashen Afrika dake Kudu da Sahara sun fi fama da matsalar yi wa ‘yan mata auren wuri a duniya. Amma wata da aka yiwa auren wuri ta samu guduwa, da wasu sauran rahotanni.
A cikin shirin na wannan makon, a Najeriya, matsalar sace dalibai daga makarantunsu da ake ci gaba da samu ta na neman kassara sha’anin ilimi a Arewacin kasar, da wasu sauran rahotanni.
Ga alama matsayar da kungiyar Jama’atu Nasaril Isalam akan mukabala tsakanin Malaman Kano da Malam AbdulJabbar na kokarin mayar da hannun agogo baya ga shirye-shiryen gwamnatin jihar na gudanar da wannan makabala.
Masana harkokin tsaro sun koka dangane da yawan mutanen da aka yi garkuwa da su domin neman kudin fansa a wannan shekara ta 2021. Bisa kiyasi, daga watan Janairun 2021 zuwa karshen Fabarairu, an sace mutun sama da 1,000.
Amurka na gab da samun mace-mace rabin miliyan sakamakon cutar COVID-19, da karin mace-mace da ke da alaka da coronavirus fiye da kowacce kasa, a cewar cibiyar samar da bayanan coronavirus ta Jami’ar Johns Hopkins.
Kamar yadda yakan faru duk bayan zaben Shugaban kasa, yau ma za a rantsar da zababben Shugaban kasa Joe Biden da Mataimakiyarsa. Kamala Harris, a wani bukin da zai sha banban da yadda aka saba yi.
Domin Kari