Rahoton Asusun Tallafa wa kananan Yara na Majalissar Dinkin Duniya, wato UNICEF dai ya nuna cewa cikin hare-haren 'yan bindiga a makarantu guda 25 a Najeriya, jihar Kaduna ce ke kan gaba.
Masu nazari kan harkokin tsaro irin su Manjo Yahaya Shinko mai ritaya na ganin matsayin gwamnatin jihar Kaduna kan 'yan bindigar na cewa gwamnati ba zata biya kudin fansa ba shi ya tunzura yan bindigar ya sa ake samun hauhawar hare-hare a jihar
Makarantu a jihar Kaduna dai sai da suka dade a rufe cikin wannan shekara kuma matsalar hare-haren 'yan bindiga ta sa aka rufe su, kamar dai yadda kwamishinan ilimi a lokacin, Dakta Shehu Usman Muhammad Makarfi, ya nuna. Ya ce jami’an tsaro sun bada shawarar rufe makarantu don tsare lafiyayar dalibai har sai wani lokaci.
Har yanzu dai dalibai da iyayen yara da dama na cike da fargaba na yanayin tsaro musamman ma a makarantun da ke nesa da gari, inji shugaban kungiyar iyayen yara ta kasa (P.T.A), Alh. Haruna Danjuma. Ya kuma ce lamarin ya jawo koma baya wajen neman gurbin zuwa makarantun kwana.
Matsayin gwamnatin jahar Kaduna kan 'yan bindiga dai shine ba sulhu kuma gwamna Nasiru Ahmed El-rufa'i ya ce jami'an tsaro na kokari, ya ce gano tsare-tsaren ta’addanci da su ke yi shi ke dakile wasu abubuwan.
Maganar matsalar tsaro na cikin manyan batutuwan da suka kawo koma baya musamman a Arewachin Najeriya, sai dai kuma gwamnonin yankin na da ra'ayin cewa su na iyaka kokarin kawo karshen matsalar baki daya.
Saurari rahoton Isah Lawal Ikara.