Rabon da tawagar mata ta Najeriya ta je gasar tun shekaru 16 da suka gabata.
Karawar da za ta fi daukan hankali za a yi ne tsakanin Real Madrid da Manchester City mai rike da kofin a ranar Talata inda City za ta bi Madrid Santiago Barnebeu.
A jihar New York, hazo ya dan kawo cikas ga masu kallon kusufin amma a jihar Texas da sauran wuraren da lamarin ya auku, an ga kufusin na dan wasu mintina yayin da wata ya ratsa ta tsakanin rana da duniyar dan adam.
“Za a ci gaba da azumi har zuwa Talata, 9 ga watan Afrilun shekarar 2024 a matsayin kwana na 30 a watan Ramadan, karamar sallah kuma za ta kasance ranar 10 ga watan Afrilu.”
Kasa da sa’a 24 bayan fitar da sanarwar da hedkwatar tsaron Najeriya ta yi, basaraken, Clement Ikolo ya mika kansa ga rundunar ‘yan sandan jihar Delta inda ya ce ba shi da hannu a kisan sojojin.
Biyo bayan umurnin shugaba Tinubu na gaggauta ceto daliban Kuriga sama da 280, babban hafsan tsaron Najeriya Janar Christopher Musa ya ce sojoji sun dukufa wajen ganin an ceto daliban da kuma hukunta ‘yan bindigan da ke wannan aika-aika, da wasu rahotanni
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce gwamnati ba za ta biya kudin fansa ba.
Atiku ya yi kiran ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook inda ya ce yin rufa-rufa kan lamarin da kuma dakatar da wanda ya kwarmata zancen ba mafita ba ce.
Taken wannan shekara shi ne “kwadaitar da jama’a” wajen mayar da hankalinsu kan al’amuran da suka shafi saka mata a harkokin yau da kullum.
A ranar 1 ga watan Maris din shekarar 2024, Babban Kwamandan Hisbah, Sheikh Daurawa ya yi murabus daga mukaminsa kan kalaman na gwamna Abba Kabir Yusuf wadanda suka soki ayyukan da Hisbah ke yi.
Akeredolu ya rasu a kasar Jamus a ranar 27 ga watan Disambar bara bayan fama da rashin lafiya. Shekarunsa 67.
NLC ta ce za ta shiga yajin aikin a ranakun 27 da 28 na wannan wata na Fabrairu don jan hankalin hukumomi kan yadda ‘yan Najeriya ke fama da matsin rayuwa.
Hukumar kula da gidajen yari a Rasha ta fada a wata sanarwa cewa Navalny ya kamu da rashin lafiya bayan da ya dawo daga wani dan tattaki da ya yi don mike kafa, inda daga baya ya yanke jiki ya fadi.
A cewar shugaban na Najeriya, za a rika karanta wannan alkawari na nuna biyayya ga kasa (National Pledge) a tarukan gwamnati da sauran taruka da jama’a suka shirya.
Kyaftin din Super Eagles, Ahmed Musa ne ya jagoranci tawagar ‘yan wasa na Najeriya yayin zaman nuna jimamin inda aka yi tsit na dan wani lokaci don yi wa mamatan addu’a.
Domin Kari