Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ranar Laraba Za A Yi Karamar Sallah - NSCIA


Jinjirin wata (Hoto: by Hussein F)
Jinjirin wata (Hoto: by Hussein F)

“Za a ci gaba da azumi har zuwa Talata, 9 ga watan Afrilun shekarar 2024 a matsayin kwana na 30 a watan Ramadan, karamar sallah kuma za ta kasance ranar 10 ga watan Afrilu.”

Majalisar kula da sha’anin addini Islama a Najeriya (NSCIA) karkashin jagorancin Mai Martaba Sarkin Musulmi, Sultan Muhammad Sa’ad Abubakar ta ce ba a ga watan Shawwal ba.

Cikin wata sanarwa da ta fitar a shafukan sada zumunta a ranar Litinin dauke da sa hannun mataimakin babban Sakatare-Janar na majalisar, Farfesa Salisu Shehu, majalisar ta ce ba a samu wani rahoto da ya nuna an ga watan na Shawwal ba.

Hakan na nufin sai a ranar Laraba za a yi karamar Sallah kuma za a cika azumi 30 maimakon 29 a cewar majalisar.

“Za a ci gaba da azumi har zuwa Talata, 9 ga watan Afrilun shekarar 2024 a matsayin kwana na 30 a watan Ramadana, karamar sallah kuma za ta kasance ranar 10 ga watan Afrilu.”

Bisa shari’ar Islama, ana sallar Eid-al-Fitr ne idan an ga watan Shawwal, wanda ke biye da watan na Ramadana.

Gabanin fitar da sanarwar da majalisar ta NSCIA ta fitar a Najeriya, su ma hukumomin Saudiyya sun sanar da Laraba a matsayin ranar sallah karama bayan da aka gaza ganin watan.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG