Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bagudu Ya Jaddada Matsayarsa Ta Jagorantar Ceto Daliban Kebbi


Gwamna Abubakar Atiku Bagudu (Facebook/Gwamnatin Kebbi).
Gwamna Abubakar Atiku Bagudu (Facebook/Gwamnatin Kebbi).

A ranar 17 ga watan Yuni, ‘yan bindiga suka far wa makarantar sakandaren ta Yauri suka sace dalibai da dama da wasu malamansu. 

Gwamnan jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin Najeriya, Abubakar Atiku Bagudu, ya kara tabbatar da shirinsa na jagorantar gayyar ceto daliban sakandaren FGC Yauri da ‘yan bindiga suka sace.

A ranar 17 ga watan Yuni, ‘yan bindiga suka far wa makarantar sakandaren ta Yauri suka sace dalibai da dama da wasu malamansu.

Sama da wata guda har yanzu babu duriyarsu.

Yayin wani taron tabbatar da wanzuwar zaman lafiya a ranar Lahadi, wanda aka saba yi hade da Fulani, jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki a harkar tsaro, gwamna Atiku ya ce ba a zabe su don su zauna a ofis ba.

Karin bayani akan: Abubakar Atiku Bagudu​, Fulani, daliban, ‘yan bindiga, Yahaya Sarki, jihar Kebbi, Nigeria, da Najeriya.

“Ba an zabe mu ba ne don mu rika zama a ofis kadai, sai don mu yi iya bakin kokarinmu wajen kare rayukan jama’a da dukiyoyinsu.” Atiku ya ce cikin wata sanarwa da kakakinsa Yahaya Sarki ya fitar.

A ‘yan makonnin da suka gabata, Atikuu ya fadawa taron maharban jihar da suka ziyarce shi cewa, zai shige gaba wajen fafutukar da ake yi ta ceto daliban.

“Ya zama dole mu yi duk abin da za mu iya wajen tabbatar da zaman lafiya, hadin kai da tsaro, ko da ta kama za mu rasa rayukanmu ne kamar yadda addini ya ambata.”

Gwamnan ya kuma yi Allah wadai da wasu “baragurbi kalilan da ke cikin al’umar Fulani, wadanda suka zabi yin fashi da makami, suke bata sunan Fulani masu son zaman lafiya a Najeriya.”

XS
SM
MD
LG