An yi kira ga 'yan takarar da su rika sanya ido akan wadanda suka nada a mukamai domin su tabbatar da cewa sun rike amana.
Gwamnatin jihar Jigawa ta ce ta na ci gaba da aikin tantance mutanen da annobar ambaliyar ruwa ta shafa a jihar domin basu tallafin daya kamata da nufin rage radadin rayuwa da suke ciki.
Mutanen da ambaliyar ruwa ta lalata musu gonaki da gidaje a jihar Kano da ke Najeriya na ci gaba da korafi kan yadda hukumomin jihar da-ma na tarayya suka yi watsi da makomar su.
Baya ga farfaganda, dukkanin jami’iyyun sun bullo da tsarin ganawa ta musamman ga muhimman rukunan jama’a, wa lau a shiyya ko jiha.
Gabanin gudanar da gangamin neman kuri’a a jihar Kano yau Laraba, a jiya Talata dan takarar shugabancin Najeriya a karkashin Jam’iyyar APC mai mulki, Bola Ahmed Tinubu ya gana da kungiyoyin malaman musulmi na yankin arewa maso yammacin Najeriya.
Hukumar dake yaki da fatauci da shan miyagun kwayoyi a Najeriya NDLEA, ta ce shigar mata, musamman masu aure cikin harkokin shaye-shaye na daga cikin manyan kalubale da take fuskanta wajen gudanar da ayyukanta a jihar Kano.
Hukumar EFCC mai yaki da yiwa tattalin arziki zagon kasa a Najeriya tace yawan sauya wa alkalai wuraren aiki da Odar da alkalan kan bayar barkatai a yayin shari’u, na daga cikin kalubalen da take fuskanta wajen gudanar da ayyukanta.
Kungiyoyin kula da harkokin addinin Musulinci na ci gaba da bayyana matsayar su dangane da hukuncin babbar kotun shari’ar Musulicin ta Kano game da shari’ar da ka yi wa Malam Abduljabbar Nasiru Kabara.
An kammala taron bita da kara wa juna sani na yini uku a Kano ga kwamandoji da sauran manyan Jami’an hukumomin Hisbah na jihohi 6 a arewa maso yammacin Najeriya.
An fara taron bita da karawa juna sani na yini uku a Kano, ga kwamandoji da sauran manyan Jami’an Hisbah na jihohi 6 dake arewa maso yammacin Najeriya da nufin neman dabaru da hikimar tunkarar kalubalen zamantakewar gida da cin zarafin mata da kananan yara.
A wani mataki na dakile akidar yanayin siyasa, kwamitin tabbatar da zaman lafiya na jihar Kano da hadin gwiwa da hukumar NBC sun gudanar da taro na musamman da shugabannin kafofin labaru da kuma wakilan manyan kafofin labarai na cikin gida da na ketare wadanda ke aikin tura rahotannin daga Kano.
Kwamiti wadda ke karkashin jagorancin farfesa Ibrahim Umar ya bayyana damuwa da kakkausan harshe game da yadda wasu daga cikin shugabanin siyasa a Kano ke kokarin dumama yanayi a jihar ta hanyar furta kazaman kalamai da ka iya tunzura magoya baya
Hukumar kula da ingancin kayayyaki ta Najeriya, S.O.N , tace yanzu haka Najeriyar na kokarin cika sharrudan samun rijistar shiga jerin kasashen duniya da ake damawa da su a hada-hadar cinikayayyar kayayyaki bisa manufa da tsarin kasuwanci na Halal.
Domin Kari