Yau aka shiga rana ta huku da kasancewar zauruka da harabobin majalisun dokokin jihohin Najeriya 36 a garkame, biyo bayan yajin aikin da kungiyar ma’aikatan majalisun ke yi, akan batun aiwatar da dokar tabbatar da ‘yancin gashin kai ta fuskar kudade da ma’aikata.
Kwanaki biyar da kaddamar da rigakafin cutar korona a jihar Kano da ke Najeriya, aikin na fuskantar kalubalen rashin fitowar jama’a.
Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya cika shekara guda da hawa karagar sarautar Kano, bayan sauke tsohon sarki Muhamamdu Sanusi na biyu.
Zamu duba kundin tsarin mulkin kasa, kamun a amince da tsarin sabon albashin ma'aikata.
Shugabancin kungiyar masu masana’antu ta Najeriya sun ce sun dukufa wajen wayar da kan mambobinsu game da alfanun sabuwar dokar gudanar da cinikayya ta bai daya tsakanin kasashen Afrika.
Ga alama matsayar da kungiyar Jama’atu Nasaril Isalam akan mukabala tsakanin Malaman Kano da Malam AbdulJabbar na kokarin mayar da hannun agogo baya ga shirye-shiryen gwamnatin jihar na gudanar da wannan makabala.
Gwamnatin jihar Kano ta ce shirinta na zamanantar da tsarin karatun tsangayu a jihar na ci gaba da samun nasara, duk kuwa da dinbin kalubale.
Yajin aikin da ‘yan kungiyar masu sana’ar tuka babur mai kafa uku da akafi sani da Adai-daita sahu ya gurgunta harkokin sufuri a birni da kewayen Kano.
Gwamnan Kano ya ce hakkin gwamnati ne ta samar da zaman lafiya a cikin al'umma. Hakan yasa gwamnatin Kano ta dauki mataki biyo bayan wasu kalamai na Sheikh AbdulJabar Nasiru Kabara.
Aikin rushe-rushen gine-gine da hukumar raya birane ta jihar Kano (KNUPDA) ta gudanar a ranar Asabar dinan a filin Mushe na unguwar Gwale a binrin Kano ya haifar da cece-kuce tsakanin ma’aikatar ilimi ta jihar Kano da al’umar yankin.
Jami’an tsaro a Kano sun yi kawanya a masallacin Ashabul Khafi dake Unguwar Gwale a cikin birnin Kano, wurin da Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ke gudanar da karatu.
A Najeriya wata takaddama kan mallakar wuraren ibada a birnin da kewayen Kano na ci gaba da wakana tsakanin mahukuta a matakai daban daban da kuma kungiyoyi da cibiyoyin al’uma dana addinai a jihar Kano.
Makiyaya da masana dokokin kasa sun mayar da martani ga kiran gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje na samar da dokar da zata haramtawa Fulani makiyaya shiga yankin kudancin da sunan kiwo.
Gwamnatin Jihar Kano a Najeriya na shirye-shiryen samar Jami’an tabbatar da ganin cewa Jama’a na bin sharuddan kare kamuwa da cutar coronavirus, su kimanin dubu guda, wadanda ta yi wa lakabi da darakarun COVID.
An samu nasarar sako wasu da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su.
Zaben kananan hukumomi da ya wakana a jihar Kano a ranar Asabar ya fuskanci karancin jama’a da suka fita kada kuri'a, ko da yake rahotanni sun ce zaben ya wakana cikin lumana.
Ganin yadda takwarorinsu a kudu ke ta hada hadar kasuwanci sanadiyyar zirga zirgar jiragen sama a yankunansu, 'yan kasuwa a arewacin Najeriya da masu harkoki da jiragen sama na kiran da a bar jiragen kasashen ketare su rika sauka a Filin Jirgin Saman Kasa da Kasa Na Mallam Aminu Kano.
A wani mataki da masu ruwa da tsaki su ka ce na tabbatar da nasarar zaben Kananan Hukumomi ne da za a yi a Kano ranar Asabar, an shirya ma masu sa ido kan zaben taton bita.
Tsohon gwamnan Kano Sanata Ibrahim Shekarau ya ce rashin hadin kai tsakanin gwamnatocin arewa na taka mummunar rawa wajen tabarbarewar al’amura a yankin, yayin da kungiyoyin rajin shugabanci na gari ke kokawa kan yadda sukace shugabannin arewan ba sa sauraron shawarwarin su.
Ma'aikatan Jihar Kano sun koka dangane da matakin gwamnati na rage albashin da aka biya su a watan Disamba da ya gabata, yayin da su kuma 'yan fasho suka yi korafin rashin samun fansho na wata-wata.
Domin Kari