Engr Mansur Ahmad da ke zaman shugaban kungiyar na kasa wadda aka kafa shekaru kusan 50 da suka gabata domin bunkasa harkokin masu masana’antu a Najeriya, ya ce baya ga dokar bai daya ta cinikayya tsakanin kasashen Afrika, sun kuma yi maraba da yunkurin gwamnatin Najeriya na shimfida bututun iskar gas daga Ajakuta zuwa Kano.
Tun lokaci mai tsawon gaske masu masana’antu a yankin arewacin Najeriya, musamman a Kano, ke korafi kan kalubalen sarrafa kayyaki a kamfanonin su.
Gwamnan Kano wanda ke jawabi a wurin bude sabuwar sakatariyar shiyyar Kano da Jigawa ta kungiyar masu masana’antun Najeriya wato MAN, ya ce gwamnati na daukar matakan yalwata masana’antun Kano da ruwa da kuma lantarki.