Hakan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da hukumar bunkasa ilimin fasahar sadarwa ta Najeriyar ke cewa, ta horas da matasa da dama kan amfani da fasahar sadarwa ta zamani wajen gudanar da harkokin noma.
Baya ga ayyukan ta’addancin mayakan Boko Haram a yankin arewa maso gabas, matsalar satar mutane domin karbar kudin fansa ita ce ta mamaye yankin yamma na arewaci da kuma yankunan tsakiyar Najeriya da sauran miyagun ayyyukan bata gari.
Kazalika ayyukan ta’adanci na ‘yan kungiyar IPOB na ci gaba da wakana a yankin kudu maso gabashin kasar.
Galibin miyagun ayyukan nan sun fi kamari a yankunan karkara, lamarin da kungiyar manoman Najeriya ke cewa, ‘ya yan ta ba sa iya zuwa gonakin su domin ayyukan noma.
Hakan dai na zuwa ne a dai dai lokacin da hukumar bunkasa ilimin fasahar sadarwa ta Najeriya NITDA ke cewa, ta horas da dinbin matasa a karkashin shirinta na bunkasa ayyukan noma ta hanyar amfani da fasahar sadarwa ta zamani.
Sai dai baya ga kalubalen tsaro, kungiyar manoman ta Najeriya ta ce akwai matsalar kidayar manoman kasar da kuma nau’ikan amfanin gona da suke nomawa.
Saurari cikakken rahoton a sauti: