Cibiyar MassChallenge dake jihar Boston a kasar Amurka dake ayyukan bincike da jagoranci da kuma tallafawa matasa masu bisirar kirkire-kirkire a fannin ilimin fasahar sadarwa ta zamani a kasashe duniya daban daban da nufin bunkasa tattalin arziki ta yin amfani da ilimin fasahar sadarwa.
Hajiya Hadiza Umar dake zaman kakakin hukumar ta NITDA ta yi Karin bayani game da yarjejeniyar da cibiyar Masschallenge, inda ta ce suna so ne Najeriya ta zama jagora a harkokin fasahar sadarwa a nahiyar Afirka, ta hanyar samarwa da matasa cibiyoyin nazari da bincike akan harkokin ilimin fasahar sadarwa.
Haka kuma, Hajiya Hadiza ta ce ana so a karfafa gwiwar matasa masu basira a wannan fanni domin samu hanyar hada su da kamfanonin da zasu tallafa mu su.
Hakan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da ‘yan Najeriya ke cewa ya kamata hukumar ta NITDA ta warware wasu kalubale da suka shafi ayyukan ta.
Inda matasa ke ganin akwai bukatar warware wasu hanyoyin da matasan za su iya bi domin amfani da ayyukan hukumar NITDA, tare da bunkasa wasu shirye-shiryenta ta hanyar da mafi yawan matasa za su mora.
Ga alama dai hankalin ‘yan Najeriya na kara karkata akan aikace aikacen wannan hukuma ta NITDA la’akari da ci ga da tasirin da ilimin fasahar sadarwa ke yi ga rayuwar su ta yau da kullum.
Domin karin bayani saurari rahotan Mahmud Ibrahim Kwari.