A wata sanarwa da gwamnatin jihar Kaduna ta fitar a yammachin jiya Talata, ta ce wasu yara ne su ka tsinto wasu abubuwa inda a garin wasa su ka fashe har su ka jikkata yara bakwai. Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Malam Samuel Aruwan ya yi wa Muryar Amurka karin bayani ya na mai cewa abin da ya fashe ba bam bane, amma wani abu me mai kama da nakiya.
Kwamishainan ya kara da cewa, yaran su bakawai suna nan a asibiti inda ake jinyarsu kuma ana samun biyan bukata.
Wani mutum Alh. Dayyabu Kerawa daya daga cikin kansilolin Karamar hukumar Igabi kuma abokin mahaifin yaran da wannan fashewa ta shafa ya ce abun ya zo da sauki.
To shin ko dama jami'an tsaro kan zubar da irin wadannan abubuwa masu fashewa? Wannan ce tambayar da muka yi wa masanin harkokin tsaro, Manjo Mohammed Bashir Shu'aibu Galma mai ritaya inda ya ce ba haka ba ne, amma gwamnan ya sa ayi bincike kuma suna kokarin dubawa.
Wannan dai ba shi ne karon farko da aka sami irin wannan fashewa cikin 'yan kwanakin nan ba, Domin kuwa a jihar Zamfara ma an sami fashewar da ta yi sanadin kashe wasu yara.
Saurari rahoton cikin sauti daga Isah Lawal Ikara:
Karin bayani akan: Jihar Kaduna, harin bam, Nigeria, da Najeriya.