Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dokar Hana Zirga Zirga Na Ci Gaba Da Aiki A Kaduna


Gwamnan Jihar Kaduna Nasiru El Rufai.
Gwamnan Jihar Kaduna Nasiru El Rufai.

Gwamnatin jihar Kaduna dake arewacin Najeriya ta kafa dokar hana zirga zirga ta sa’o’i 24 a cikin jihar, lamarin da yasa shugabannin addinai suka bayyana rashin amincewar su da wannan mataki da gwamnatin jihar ta dauka, suna cewa ba a kai ga wannan matsayi ba tukuna.

Matakin da gwamnatin jahar Kaduna na zuwa biyo bayan da matasa suka kai hare hare a wasu wurare da aka adana kayan abinci na tallafin coronavirus da magunguna da hukuma ta kwace daga masu safarar su kana aka sace kayan masu tarin yawa. Gwamnatin ta ce da yawan kayan tallafin da aka sace na da hadari ga rayuwar wadanda su ka yi amfani da su.

Jami'an gwamnatin Kaduna wadanda su ka zagaya wuraren da aka balle don dibar kayan tallafi da na wasu hukumomi sun ce cikin kayan da aka sace har da magungunan da ake dab da konawa da kuma wani waken soya da aka sa mai maganin kwari.

Dokar hana zirga-zirga ta sa'oi ashirin da hudun da gwamnatin Kaduna ta saka dai ba ta sami karbuwa gurin kungiyar Kiristocin Najeriya wato CAN reshen jahar Kaduna ba. Shugaban CAN Rabaran Joseph John Hayep ya ce sun yi Allah wadai da wannan matakin gwamnati, saboda kafin a dauki matakin hana zirga zirga sai abu ya kai matuka amma ba irin wanda za a iya magancewa cikin sauki ba.

A nahi bayanin, sakataren majalisar malamai da limamai ta jihar Kaduna Malam Yusuf Yakub Arrigasiyyu, yace ya kamata duk abin da ake bukata a neme shi ta hanyar sulhu amma kada a yi abinda zai kawo wa mutane tashin hankali.

Har cikin daren jiya Lahadin da Mataimakiyar gwamna ta yi jawabi ga al'umar Kaduna dai, gwamnati ba ta sassauta dokar hana zirga-zirga ba amma kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida Mal Samuel Aruwan ya ce an kama mutum kimanin 11 da aka same su da kayan mutane.

Wasu al'umar Kaduna dai sun dage kan cewa idan bera da sata to daddawa ma da wari. Sun ce abin da matasan suka yi bai dace ba amma kuma bai yiwuwa ga abinci a bar mutane da yunwa dole za a samu rikicki.

Saurari rahoton Isah Lawal Ikara cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:19 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG