Gidan Tarihi na arewa dake Kaduna a Arewacin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari bayana tarihi a matsayin sinadarin cigaban kowacce al'umma.
Shugaban Kasa, wanda ministan ruwa, Injiniya Suleiman Adamu ya wakilta a wajen taro cikar gidan Tarihi na Arewa House Shekaru hamsin da kafawa, ya taya cibiyar murna, ya kuma bayana alfaharin gwamnatin tarayya ganin yadda aka samu ci gaba sosai a cikin wadannan shekaru.
Ya bayyana muhimmancin wannan cibiyar da kuma yaba yadda aka yi aiki ba dare ba rana aka tattara bayanai don inganta cibiyar kanta da kuma tattara bayanai akan tarihin arewa. Hakan yana tunatar da mutane tarihinsu, domin “Idan baka san daga inda ka zo ba, idan baka san tarihin ka ba to baka san inda ka dosa ba.”
Shugaban kungiyar gwamnonin jamiyyar APC mai mulki a Najeriya kuma gwamnan jahar Kebbi Alhaji Atiku Abubakar Bagudu, ya ce duk da ya ke an sami cigaba amma har yanzu akwai aiki a gaba.
Maganar hadin kan kasa na daga cikin abubuwan da aka tattauna akai a wajen wannan taro kuma ta dauki hankalin gwamnan jahar Jigawa Mohd Badaru Abubakar.
Gwamna Badaru Abubakar ya bayana farinciki da aka dau wannan batu a matsayin abun da za’a tattauna akai ganin cewa abu ne da marigayi Sardaunan Sakkwato Sir Ahmadu ya ginu akai, na hadin kan mutane da hadin kan kasa. Yayi fatan ganin hakan zai shiga cikin zuciyar al’umma domin ingantaa zamantakewa a tsakanin mu a wnnan kasa tamu.
Dr. Shu'aibu Shehu Aliyu Daraktan gidan tarihi na Arewa House da ake kira gidan Sardauna ya ce wannan cibiya ta ta’allaka ne wajen hada kan arewa tare da Najeriya baki daya. Ya kara da cewa daya daga cikin irin wannan kudiri shi aka gayyato Gwamnan Ekiti kuma shugaban gwamnonin Najeriya Kayode Fayemi ya gabatar da kasida akan “abun da za’ayi akara dinkewa, kuma akara dunkulewa a fadin kasan nan, a kuma kwakulo kalubale da abubuwan da ke yi mata bara zana don magancesu.
Tsohon mataimakin shugaban Kasa Alhaji Mamadi Mohammed Sambo, da mai-alfarma Sarkin Musulumi Sa'ad Abubakar, da Shugaban gwamnonin Najeriya kuma gwamnan Ekiti, Kayode Fayemi na daga cikin manyan bakin da su ka halarchi wannan taro na cika Shekaru hamsin da kafuwar gidan Sardauna, wato Arewa House dake Kaduna.
Saurari cikakken rahoton Isa Lawal Ikara cikin sauti:
Facebook Forum