Hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya INEC ta jaddada kudirinta na aiki tare da sauran hukumomin tsaro da masu ruwa da tsaki don dakile yawan amfani da makudan kudade da 'yan siyasa ke yi a lokacin gangamin yakin neman zabe dama sayen kuri’u a lokacin babban zaben kasar mai gabatowa a 2023.
Wasu ‘yan kasuwan sun ce ba za su iya rage kayan ba saboda a lokacin da suka siyo kayan dala na sama akan cedi.
A ci gaba da fama da hare haren 'yan bindiga da 'yan arewacin Najeriya ke fuskanta wani sa'in a kudancin Najeriya, wannan karon sun auna wani masallaci a jihar Delta.
Kwamiti wadda ke karkashin jagorancin farfesa Ibrahim Umar ya bayyana damuwa da kakkausan harshe game da yadda wasu daga cikin shugabanin siyasa a Kano ke kokarin dumama yanayi a jihar ta hanyar furta kazaman kalamai da ka iya tunzura magoya baya
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Adamawa CP Sikiru Akande ya tabbatar da kama wadansu mutane da ake zargi da garkuwa da mutane da kuma aikata miyagun laifuka a jihar.
‘Yan Najeriya sun yi Allah wadai game da tasa keyar wani dalibi da ake zargi ya caccaki uwar gidan shugaban kasar Najeriya Aisha Buhari a kafar sadarwa ta Tiwita zuwa gidan yari,
Jamus ta gujewa wani abin kunya na ficewa daga gasar cin kofin duniya a farkon gasar a lokacin da suka tashi kunnen doki 1-1 da Spain a ranar Lahadi, inda Niclas Fuellkrug ya farke kwallon da ya ci a minti na 83 da fara wasa.
Wales dai ta samu bugun fenariti ne, bayan da Walker Zimmerman ya kwade Bale ta baya, kuma alkalin wasa Abdulrahman Al-Jassim na kasar Qatar mai masaukin baki, bai yi wata-wata ba ya nuna bugun daga kai sai mai tsaron gida.
Shirin ya ta'allaka ne kan rikicin rushewa wasu mutane gininsu da suka ce an yi a jihar Bauchi da ke arewa maso gabashin Najeriya.
Ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya ce akwai yiwuwar kai Harin ta'addanci a Najeriya, musamman Abuja.
A wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta, wasu 'yan ta'adda sun yi barazanar tilasta wasu 'yan mata biyu 'ya'yan tsohon Akanta-Janar na Zamfara yin aikin ta'addanci tare da su.
Wasu likitoci 'yan asalin Najeriya da suka koma aiki da asibitocin Turai sun koka kan yadda ake mayar da su tamkar bayi a Burtaniya.
Idan an tuna, a makon jiya mun cigaba da tabo halin tsaka mai wuya da Funali ke ciki a Najeriya sanadiyyar yawan zarginsu da aikata wasu laifuka. A daya bangaren kuma, su ma su na zargin cewa akan kuntata ma su bisa zato kawai. Yau ma za mu dora a kai.
Domin Kari