Rundunar ‘Yan sandan jihar Adamawa ta cafke masu garkuwa da mutane da kuma wasu masu manyan laifuka su dari da tara. Ta kuma kwace bindigogi kirar Ak47 da kirar hannu guda 48 a hannun 'yan bindiga.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Adamawa CP Sikiru Akande ne ya tabbatar da hakan da yake jawabi a wurin taron manema labarai a shalkwatar ‘yan sandan Jihar.
A hirar shi da Muryar Amurka, Yusuf Hamedu daya daga cikin wadanda aka kama da laifin garkuwa da mutane ya ce mutane biyu su ka yi garkuwa da su.
Ya kuma bayyana cewa, sun karbi miliyan goma a wurin daya, yayinda suka karbi miliyan uku a wurin dayan.
Wani daga cikin mutanen da aka kama mai suna Hassan Alhaji Jiddo ya bayyana cewa, hada baki su ka yi da wasu su kashe yayyensa guda biyu a karamar hukamar Song dake Jihar Adamawa.
A nashi bayanin, wani mai suna Nafi’u Buba ya bayyana cewa, da matarsa suke garkuwa da mutane a wani yanki na Jihar Adamawa, daga bisani ‘yan sanda suka kamo su gaba daya inda yanzu haka zasu fuskaci shari’a a gaban kotu.
Masu manya manyan laifukan da aka gabatar wa ‘yan jaridun sun hada da masu garkuwa da mutane, da masu satar shanu da dai sauransu.
Saurari rahoton Lado Salisu Garba cikin sauti: