Shugaban sojojin Mali Assimi Goita ya fada a ranar Talata cewa ya tattauna ta wayar tarho da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin game da halin da ake ciki a Nijar, inda sojoji suka kwace mulki a wani juyin mulki a watan jiya.
Kiristoci daga Najeriya, Nijar da Chadi sun shafe kwanaki bakwai suna gudanar da addu'o'i ga kasar ta Nijar dama Nahiyar Afrika baki daya.
Wannan sabuwar dambarwa ta kunno kai ne kwana guda bayan da wata tawagar manyan malaman addinin Islama daga Najeriya ta kai ziyarar shiga tsakani a rikicin siyasar kasar.
Sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar sun ce za su tuhumi hambararren Shugaban kasar Mohamed Bazoum da laifin “cin amanar kasa” da kuma yi wa sha’anin tsaron kasa zagon kasa.
Wata tawagar malaman addinin Islama ta ziyara a birnin Yamai a ranar Assabar inda suka gana da shugabannin mulkin sojin jamhuriyar Nijar da suka hada da Janar Abdourahamane Tchiani da Firai Minista Ali Mahaman Lamine Zeine.
Sai dai bikin na bana ya zo ne a daidai lokacin da jihar Filato ke fama da matsalar tsaro.
Wasu 'yan Nijar na ganin Faransa ba ta tabuka wani abin a-zo-a-gani a yakin da take yi da ayyukan ta'addanci a kasar da ma yankin Sahel baki daya.
Sabuwar gwamnatin ta rikon kwarya wacce Firai Minista, kuma Ministan kudin kasa Ali Mahaman Lamine Zeine zai jagoranta na da mambobin 21
Yayin da wa’adin rufe rijistar dalibai na bana a Jami’ar Bayero Kano ke cika, kungiyar tsoffin daliban Jami’ar lokacin tana karkashin Jami’ar Ahmadu Bello ta Zaria, ta shiga tsakani.
Kungiyar ta Shi'a ta bayyana matsayarta ne yayin da shugabannin kasashen kungiyar ta ECOWAS ke taro a Abuja don duba mataki na gaba da za su dauka.
Tun kafin isowar damunar, hukumar hasashen yanayi ta Najeriya ta yi gargadin samun ambaliyar ruwa a kananan hukumomi da dama na kasar a ciki har da na jihohin Nejan.
Dubban mazauna Hawaii ne suka dinga tserewa daga gidajensu a Maui yayin da wata gobara ta mamaye tsibirin, inda ta lalata sassan wannan gari da ya shafe shekaru aru-aru tare da kashe akalla mutum 36 a wata gobarar daji mafi muni da Amurka ba taba gani ba a shekarun baya-bayan nan.
Kwararru da masana na ci gaba da zakulo abubuwan da su ke ganin ka iya zama dalilan da, zuwa yanzu, suka hana amincewa da sunan tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasuru Ahmed El-rufa'i a matsayin Ministan Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar sun zargi kasar Faransa ta kai hari kan wasu askarawan kasar da sanyin safiyar yau Laraba 9 ga watan Agusta a wani kauyen Jihar Tilabery, abin da ya haddasa asarar rayuka, koda yake kawo yanzu ba a tantance adadinsu ba.
Hambararren Shugaban Nijar na fuskantar karancin abinci kuma ya na fama da wasu munanan yanayoyi, makwanni biyu bayan hambarar da shi a wani juyin mulkin da sojoji suka yi masa tare da tsare shi, kamar yadda mai ba da shawara ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Associated Press a yau Laraba.
Domin Kari