NIAMEY, NIGER - Ganawar dai na da nufin share fage na shirye-shiryen zaman sulhu a tsakanin kungiyar kasashen Afrika ta yamma ECOWAS da sojojin da suka kifar da shugaba Mohamed Bazoum daga karagar mulki.
Malaman addinin kusan 20 daga dariku da akidu daban-daban ne suka ziyarci birnin na Yamai a da zummar neman hanyoyin kusanto banagrorin da ke takaddama sanadiyar juyin mulkin da soja suka yi a ranar 26 ga watan Yulin 2023.
Tawagar a karkashin jagorancin shugaban kungiyar Izatul bidi’ah wa ikamatu sunnah, Sheik Abdullahi Bala Lau, haka ma ta nemi ganawa da Shugaba Mohamed Bazoum a inda ake tsare da shi sai dai haka ba ta ta cimma ruwa ba, kamar yadda Malan Aminu Sheik Dahiru Usman Bauchi ya shaidawa Muryar Amurka.
Firai Ministan rikon kwarya Ali Mahamane Lamine Zeine ya jaddada aniyar gwamnatinsa na zama akan teburin sulhu duk da yake ECOWAS ta kakaba wa Nijar takunkumi ba akan ka’ida ba inji shi.
Baya ga tankiyar siyasar da juyin mulkin ranar 26 ga watan yuli ya haifar a tsakanin Majalisar CNSP da kasashen duniya, a can cikin gida wasu ‘yan kasar na fakewa da zanga-zangar goyon bayan juyin mulkin don tafka ta’asa, lamarin da ya sa mai masaukin baki Sheik Abubakar Shehu Usman Sanam jan hankulan masu wannan danyen aiki.
Shugaba Mohamed Bazoum wanda a farkon mako bayanai suka yi nuni da cewa shi da iyalinsa na tsare cikin halin irin na muzantawa sakamakon rashin wutar lantarki da ruwa har ma da karincin abinci, ya samu ziyarar likitansa a cewar wasu rahotanni a ranar Assabar, wadanda suka kara da cewa likitan ya je masa da guzirin abinci, haka kuma ya ba da albishirin cewa babu wata alamar zullumi a tattare da Shugaban.
Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:
Dandalin Mu Tattauna