Al’ummar birnin Derna da ke gabashin Libya sun binne mutane 700 da suka mutu sakamakon mummunar ambaliyar ruwa, kuma wasu 10,000 sun bace a yayin da ma'aikatan ceto ke kokarin gano karin gawarwaki da dama daga mummunar ambaliyar ruwa da laka, in ji jami'ai a yau Talata.