Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hedkwatar ‘Yan Sandan Najeriya Ta Kafa Wani Kwamiti Don Sake Duba Tsarin Mallakar Bindiga


ACP Muyiwa Adejobi
ACP Muyiwa Adejobi

Wata sanarwa da kakakin hedkwatar ‘yan sandan Najeriya ACP Muyiwa Adejobi ya aika wa Muryar Amurka a Abuja, ta ce an dora wa sabon kwamitin alhakin bitar dokoki da matakan da ake bi wajen sahalewa mutane ikon tu'amali da bindigogi.

Adejobi ya ce za a dauki matakin ne daidai da tanaje-tanajen kundin tsarin mulki kan mallakar bindiga domin kare muradi da tsaron al'umma baki daya.

A kokarin yin hakan a cewar sanarwar, za a ji ta bakin kwararru, kungiyoyi masu zaman kansu, da sauran masu ruwa da tsaki don tabbatar da an fito da tsari mai cikakken inganci da kowa zai yi na'am da shi.

Babban baturen ‘yan sandan Najeriya IGP Kayode Egbetokun, ya ce a wannan karon za a yi nazari a tsanake don ganowa tare da tantance irin ka'idojin da a halin yanzu ake bi wajen bayar da lasisin mallakar bindiga.

Tuni dai masana tsaro irin su Dr. Kabiru Adamu ke ganin wannan matakin yayi daidai, to amma akwai bukatar rundunar 'yan sandan ta yi aiki tare da sauran hukumomin gwamnati musamman wadanda aka dora wa alhakin shawo kan bazuwar makamai a kasar, da ke karkashin ofishin mai bai wa shugaban kasa shawara kan sha'anin tsaro.

Shi ma mai bibiyar matsalolin tsaro Basharu Altine Guyawa Isa, da ke ganin kamar an makaro, a daya hanun na mai cewa lallai duk da haka motsi ya fi labewa, duba da irin barnar da makaman da ke hanun jama'a ba bisa ka'ida ba ke yi.

Saurari cikakken rahoton Hassan Maina Kaina:

Hedkwatar ‘Yan Sandan Najeriya Ta Kafa Wani Kwamiti Don Sake Duba Tsarin Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:25 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG