A jawabin da ya gabatar gaban zauren Majalisar Dinkin Duniya ranar Talata a birnin New York, shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ce yana neman sake maido da tsarin dimokradiyya a Nijar don magance matsalolin siyasa da na tattalin arziki da suka dabaibaye makwabciyar kasar bayan juyin mulki.
Sama da kananan yara 1,200 ne suka mutu sakamakon cutar kyanda da tamowa a sansanonin ‘yan gudun hijirar Sudan, yayin da wasu dubbai da suka hada da jarirai ke fuskantar barazanar mutuwa kafin karshen shekara, in ji hukumomin Majalisar Dinkin Duniya a ranar Talata.
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya tattauna da shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa a birnin New York da ke Amurka, don neman fadada hadin gwiwar tattalin arziki tsakanin kasashe biyu masu karfin tattalin arziki a Afirka, in ji kakakinsa ranar Litinin.
Muryar Amurka ta tattauna da wani mai fafutuka da sharhi a Najeriya, Nastura Ashir Sharif ta Skype, inda muka ji ra’ayin shi a game da tallafin rage radadin a wannan lokaci.
Majalisar dokokin Ghana ta amince da wani kudurin doka da za ta haramta zargin mutane da maita. Idan kudurin ya zama doka, zai tilasta rufe sansanonin da mutanen da ake zarga da maita suke zuwa neman mafaka don kar a halaka su.
A jihar Bornon Najeriya mutane da dama na korafin rashin yin adalci wajen rabon tallafi, inda wasu kuma ke cewa labarin ana rabon kayan abinci kawai suke ji, amma bai kai garesu ba.
A game da girgizar kasar a Morocco, Muryar Amurka ta tattauna da Farfesa Adnan Abdulhamid na Jami’ar Bayero dake Kano inda ya yi mana karin haske akan wasu dalilai da suka sa girgizar kasar a Morocco ta yi muni sosai.
Mutane da dama a sassan Najeriya su na sukar wannan shiri na raba tallafin rage radadi, inda wasu ke cewa akwai cuwa-cuwa a ciki, da siyasa, da jinkiri, sannan a wasu wuraren abin da ake ba mutane bai taka kara ya karya ba.
Babban taron Majalisar Dinkin Duniya ya hado kan shugabannin kasashen duniya a birnin New York a wannan mako, inda tarukan da za a gudanar a ranar bude taron, za su mai da hankali kan kara kaimi wajen cimma muradun samar da ci gaba a duniya.
Shugabannin sojan kasashen yammacin Afirka na Burkina Faso, Mali, da Nijar sun rattaba hannu kan wata yarjejeniyar kare juna a karshen makon da ya gabata.
Majalisar dokokin Ghana ta amince da wani kudurin doka da za ta haramta zargin mutane da maita; Mutane da dama a sassan Najeriya su na sukar shirin gwamnatin kasar na raba tallafin rage radadin rayuwa, da wasu rahotanni
Hukumar lafiya ta duniya, da kungiyar agaji ta Red Cross ta duniya da kuma Red Crescent suna kai gudummuwa a kasar Libya inda aka sami ambaliyar ruwa da ya rutsa da dubun dubatan mutane.
An samu katsewar wutar lantarki a duk fadin Najeriya a yau Alhamis bayan da tashar wutar lantarkin kasar ta tsaya sakamakon wata matsala da ta samu, kamar yadda kamfanonin rarraba wutar lantarki a yammacin Afirka suka ruwaito.
Ma'aikatan ceto na ci gaba da aiki yau Alhamis a gabashin Libya, inda wata mummunar ambaliyar ruwa ta yi sanadin mutuwar dubban mutane, wasu dubbai kuma suka bata.
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bayyana bakin cikinsa game da bala'in da ya afku a Libiya da Morocco.
Tsohon Firai Ministan Nijar Hama Amadou da ke hijira a kasashen waje ya koma gida da nufin bada gudunmowa a kokarin fitar da kasar daga dambarwar siyasar da ta biyo bayan juyin mulkin 26 ga watan Yulin 2023.
Gwamnatin mulkin sojan jamhuriyar Nijar ta ba da sanarwar yanke yarjejeniyar ayyukan soja da jamhuriyar Benin sakamakon zargin makwabciyar kasar da saba alkawari.
Bayan mako guda da jagorantar yajin aikin gargadi na kwanaki biyu a fadin kasar, Kungiyar Kwadago ta sake barazanar fara yajin aikin sai baba ta gani idan har gwamnatin tarayya ta gaza biyan bukatun ta.
Domin Kari