Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyoyin Agaji Na Duniya Sun Kai Gudunmawa Libya


APTOPIX Libya
APTOPIX Libya

Hukumar lafiya ta duniya, da kungiyar agaji ta Red Cross ta duniya da kuma Red Crescent suna kai gudummuwa a kasar Libya inda aka sami ambaliyar ruwa da ya rutsa da dubun dubatan mutane.

WASHINGTON, D. C. - A wani rahoto da Kamfanin dillancin labaran Associated Press ya wallafa yau Jumma’a an bayyana cewa, an hana farar hula shiga birnin Derna da ke gabashin kasar Libiya wanda ambaliyar ruwa ta kwashe, a kokarin da ake na ganin cewa ba a samu cikas ba ga aikin da kungiyoyin agaji ke yi na nemo mutane cikin laka da baraguzan da ke cikin birnin.

Libya
Libya

Kungiyar agaji ta Red Crescent ta Libya a jiya Alhamis ta ce adadin wadanda suka mutu sakamakon ambaliyar ruwar a birnin Derna da ya auku tun ranar Lahadi ya kai 11,300, kuma an ba da rahoton bacewar wasu karin mutane 10,100.

Kamfanin dillancin labaran ya ambaci ta bakin Ministan lafiya na gabashin Libya, Othman Abduljaleel, da ke cewa, an binne gawarwaki dubu 3, yayin da ake ci gaba da shirin yi wa wasu 2,000 jana’iza.

Derna, Libya Sept. 12, 2023.
Derna, Libya Sept. 12, 2023.

Abdulmenam al-Ghaithi magajin garin Derna, ya shaidawa gidan talabijin na al-Arabia cewa adadin wadanda suka mutu na iya kaiwa 20,000.

Derna ne yankin da lamarin ya fi muni, inda ruwan sama kamar da bakin kwarya da fashewar madatsun ruwa suka lalata gine-gine, da binne wurare a cikin laka da kuma kwashe mutane zuwa teku.

Libya's gabashin Soussa.
Libya's gabashin Soussa.

Guguwar ta kuma kashe kimanin mutane 170 a wasu sassan gabashin Libya, in ji Ministan lafiya.

Hukumar lafiya ta duniya, kungiyar agaji ta Red Cross ta duniya da Red Crescent, da kuma kungiyoyin agaji na Red Cross cikin hadin guiwa, sun fitar da sanarwar gargadi game da binne wadanda suka mutu cikin gaggawa.

Derna, Libya
Derna, Libya

Kungiyoyin kiwon lafiya sun ce sun aika da tawaga zuwa Libya don bada shawarwari da horaswa, wani lokaci kuma suna taimakwa da aikin binne mutanen da su ka mutu.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG