Akalla mutane 50 ne suka jikkata a ranar Litinin, akasarinsu da kananan raunuka, bayan da kamfanin jirgin LATAM ya shaidawa jaridar New Zealand Herald cewa ‘tangardar na'ura’ ta sabbaba wani ‘kwakkwaran motsi’ a tafiyar wani jirgin sama daya tashi daga birnin Sydney zuwa Auckland a kasar Australia.
Aljeriya na shigo da naman sa da na rago mai tarin yawa domin tunkarar yanayi bukatu na naman da ake sa ran amfani da shi a duk watan Ramadan mai alfarma, tare da fatan daidaita farashin yayin da tattalin arzikin kasar ke ci gaba da kokawa.
Falasdinawa sun fara azumin watan Ramadan kamar sauran dauniya ne a yau Litinin a daidai lokacin da watan na Mususlmi ya fara kuma babu wata tattaunawar tsagaita wuta.
Hira da wata mai fafutuka akan albarkacin zagayowar ranar mata ta duniya; a birnin Jos na Najeriya wata mata ta dukufa koyawa mata sana’o’i da karfafa su don ganin sun iya shawo kan kalubalen da zai iya hana su cimma muradunsu, da wasu rahotanni
IWD rana ce ta musamman da aka kebe a duniya domin bikin murnar nasarorin zamantakewa, tattalin arziki, al'adu, da siyasa na mata.
Ministan harkokin wajen Najeriya Yusuf Maitama Tuggar da takwaransa na Rasha Sergey Lavrov sun tattauna batutuwan da suka shafi moriyar juna da kuma zaman lafiyar yankin a birnin Moscow ranar Laraba.
Babban jami’in ‘yan gudun hijira na Majalisar Dinkin Duniya ya yi wani sabon gargadi yau Alhamis cewa sama da mutane 780,000 suka rasa matsugunansu a Mozambique, mafi yawansu saboda tada kayar baya na tsawon shekaru bakwai da kungiyar jihadi ta yi wanda ya jefa arewacin kasar cikin rudani.
Jami’an rundunar shiyyar Maiduguri na Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati, EFCC, ta kama su a ranar Talata, 5 ga wannan watan na Maris.
Rahotanni daga Ngala hedkwatar Gambarou Ngala a jihar Borno, na cewa 'yan kungiyar Boko Haram sun yi garkuwa da kimanin mutane 319.
Domin Kari