Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Mutane 42 A Wani Rikici Tsakanin Al'ummomi Biyu A Kasar Chadi


Sojojin Chadi.
Sojojin Chadi.

Wani rikici tsakanin al'umomi biyu a gabashin kasar Chadi ya yi sanadiyar mutuwar mutane 42, kamar yadda ma'aikatar tsaron jama'a ta sanar a ranar Alhamis, a wani yanki na hamada na babban yankin Sahel dake fama da takaddamar filaye.

WASHINGTON, D. C. - Ma’aikatar ba ta bayyana takamaimen wadanda ke da hannu a fadan ba, ko kuma tsawon lokacin da aka yi ba, amma a kullum yankin na ganin fadace-fadacen da ake yi tsakanin manoma da makiyaya, ko kuma wasu kungiyoyi, dangane da filaye.

A wata sanarwa da gwamnatin kasar ta fitar ta ce a sakamakon fadan an kama mutane 175 a wurin, inda wasu ‘yan bindiga suka kona wani bangare mai yawa na kauyen Tileguey da ke lardin Ouaddai.

Ministan tsaron jama'a Janar Mahamat Charfadine Margui ya shaidawa kamfanin dilancin labaren AFP a cikin wani sakon wayar tarho cewa "An shawo kan lamarin amma ana kokarin sasanta bangarorin daban-daban."

Ministan ya kasance a wurin da aka gwabza fadan, inda ya jagoranci tawagar gwamnati da sojoji da nufin ba da cikakken haske kan lamarin.

A gabashi da kudancin Chadi, inda mazauna yankin da dama ke dauke da makamai, ana ta samun rikici ne a yayin da manoma ke zargin makiyaya da barin dabbobi su yi kiwo a gonakinsu ko kuma su tattake amfanin gona.

-AFP

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG