Allah ya yi wa fitaccen jarumin fina-finan Hausa, Usman Baba Pategi, wanda aka fi sani da Samanja Mazan Fama rasuwa yana da shekaru 84 a duniya.
Kinshasa tana zargin Kigali da taimakawa ayyukan kungiyar ‘yan tawaye M23 a gabashin DR Congo, yayin da ita Rwandan ke zargin Congo da taimakawa ayyukan kungiyar ‘yan tawayenta ta Democratic Forces for Liberations of Rwanda FDLR.
Kasar Saudiyya dai na da yakinin za ta karbi bakuncin gasar cin kofin duniya ta maza ta 2034, bayan da hukumar kwallon kafa ta Australia ta janye bukatar ta wanda galibi ke ganin FIFA ta shirya lamarin don kasar mai arzikin man fetur ta samu cikin sauki.
Shugabannin kasashen duniya sun sanar da takwarorinsu matsaloli da kuma manufofinsu; Dalilai da ya sa manufofin da ake cimmawa a wajen irin wannan taro ba sa kai labari; Manufar da hukuncin kotun kararrakin zabe a jihar Kano ke nunawa, da wasu rahotanni
To a game da wannan babban taron na Majalisar Dinkin Duniya, mun samu rahotanni kai tsaye daga birnin New York yadda aka gudanar da taron
Shugabannin kasashe sama da 30 ne suka yi jawabi jiya da ke zama ranar farko da aka bude mahawara a taron kolin MDD na cikon 78 a birnin New York
An fara muhawara a Babban taron Majalisar Dinkin Duniya a helkwatan Majalisar da ke birnin New York a Amurka.
Domin Kari