Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami’an Tsaron Farin Kaya Sun Kama Wasu Matasa Da Ake Zargi Da Dabbaka Dabi'ar Auren Jinsi Daya A Gombe


Jami’an Tsaron Najeriya
Jami’an Tsaron Najeriya

Jami’an tsaro na farin kayan sun kama matasan samari maza kimanin 76 a lokacin da suka taru a wani katafaren wajen shakatawa  mai suna Duwa Plaza a garin Gombe, da zimmar gudanar da bikin zagayowar shekarar haihuwan daya daga cikinsu.

GOMBE, NIGERIA - Bayanai sun yi nuni da cewa, taron ya fake ne da bikin zagayowar shekara saboda jinsi maza da maza a lokacin sai asirinsu ya tonu.

Kamar yadda rahoto ya nuna, an kama matasan ne a lokacin suna gudanar da bukukuwan zagayowar shekarar haihuwa da kuma murnan kulla aure.

A tattaunawa da kwamandan rundunan jami’an tsaron farin kaya a jihar Gombe, Muhammed Mu'azu, ya ce sun samu nasarar kame matasan ne, sanadiyar rahoto na sirri da suka samu.

Ganin cewar ‘yan adam suna da 'yancin gudanar da abubuwan da suke so, muddin bai ci karo da dokar kasa ba, sai muka tuntubi, shugaban kungiyar kare hakkin ‘dan adam shiyyar Arewa Maso Gabas, Aliyu Muhammed Wayas, wanda ya shaida mana cewa auren jinsi a jihar Gombe walau na maza da maza ko kuma mata da mata laifi ne a jihar da ya saba doka.

Saurari cikakken rahoto daga Abdulwahab Muhammad:

Jami’an Tsaron Farin Kaya Sun Kama Wasu Matasa Da Ake Zargi Da Dabbaka Dabi'ar Auren Jinsi Daya A Gombe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:46 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG