A Najeriya 'yan awaren Biafra sun yi bukin cika shekaru hamsin da yunkurin kafa gwamnatin da ya haifar da mummunan yakin basasa a kasar.
A Faransa kuma Francois Fillon, dan takara mai matsanacin ra’ayi da ya sha kaye a zaben shugaban kasa, ya bayyana a gabanin masu binciki akan zargin cewa ya samarwa yan uwansa ayyukan bogi da ba na gaske ba.
Sai kuma a Najeriya inda aka saki Nnamdi Kanu shugaban 'yan kungiyar Biafra bayan tsarewar da aka yi mishi ta wattani 18, sai dai ya kara jadada kudurinsu na neman kasa mai cin gashin kanta.
Sojojin Japan da su ka rage sun janye daga aikin tabbatar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a Sudan Ta Kudu
Kungiyar kasashe 7 ta fara taro a Sicily. Shugaban Amurka Donald Trump ya ce batutuwan ta'addanci da Koriya Ta Arewa ne gaba a ajandar.
INDONESIA: An yiwa wasu mutane biyu bulala 82, a bainar jama’a a harabar wani masallaci a Banda Aceh, sakamakon samunsu da laifin luwadi.
ETHIOPIA/SWITZERLAND: Tsohon ministan lafiya da harkokin wajen kasar habasha Tedros Adhanom, na iya kasancewa na farko a nahiyar Afirka da zai rike mukamin shugaban hukumar lafiya ta majalisar dinkin duniya.
A can Jamhuriyar Demokratiyar Congo magoya bayan shugaban kristoci dake tsare a kurkurku sun kai hari a gidan yari, inda suka fitar da shi da kuma fursononi 50 a safiyar yau laraba.
Shugaba Vladmir Putin yayi zargin cewa yanada shaidar cewa shugaban Amurka Donald Trump bai bada bayyanan sirrin kasar Rasha ba.
Domin Kari