Wata kotu a Janhuriyar Nijar ta yankewa wani shugaban 'yan adawa hukuncin je-ka gyara-halinka na watanni 3, bayan da ya yi kiran a kifar da gwamnatin kasar.
A Iran wasu Mahara sun kai harin bindaga da na bama bamai a ginin majalisar kasar da kuma wata makabarta, inda akalla mutane 12 suka mutu wasu da yawa kuma suka jikkata. Kungiyar ISIS ta dauki alhakin harin.
Gwamnatin kasar Habasha ta yanke hanyoyin sadarwa ta kwanfuta domin ta hana masu cuwa-cuwar Jarrabawa wallafa tambayoyin akan shafunkan sada zumunta.
EGYPT: Shugaban kasar Uruguay, Tabare Vazquez, ya gana da babban Limamin jami’ar al-Azhar Ahmed al-Tayeb a Alkahira.
JAPAN: Masu binciken sararin samaniya sun kaddamar da tauraron dan’adam na biyu domin inganta ayyukan na’urar GPS ko jagoran-zamani na kasar.
An fara amffni da hangar jirgin kasa mai nisan kilomita 480, wadda ta hada birnin Nairobi da Mombasa da wani kamfanin China ya gina a Kenya.
Shugaba Donald Trump ya fidda Amurka daga yarjejeniyar canija yanayi da aka comma a Paris, yarjejeniyar da kusan kasashen Duniya suka rattabawa hannu.
Domin Kari