Russia: Rundunar Sojin Rasha ta ce watakila ta kashe Shugaban IS Abubakar Al Baghdadi a hare-haren sama da ta kai a Syria a watan Mayu amma Minista harkokin wajen Rasha Lavrov ya ce ba’a tabbatar da gaskiyar rahoton ba tukuna.
Ivory Coast: A Abidjan daruruwan masoya sun taru a filin jirgin saman Abidjan don tarbon gawar tsohon dan wasan kwallon Newcastle, Chieck Tiote mai shekaru 30 da haihuwa wanda ya fadi yayin da yake motsa jiki kuma ya cika a asibiti a makon da ya gabata a China.
Shugaba Macky Sall na Senegal da takwaransa na Faransa Emmanuel Macron sun gana a Faris, inda suka sake jaddada kudirinsiu na yaki da ta'addanci da rage dumamar yanayi.
Kungiyar da ta kama Seif Al-Islam Gaddafi, a shekarar 2011, ta sako dan na tsohon shugaba Muammar Gaddafi na Libya.
Domin Kari