Labaran duniya a cikin hotuna daga Sashen Hausa na Muryar Amurka dake birnin Washington, DC.
Hotunan Labaran Duniya na Ranar Talata 20 Ga Watan Yuni Shekarar 2017

1
Wani mai wa'azi ya durkusa yana addu'a tare da yin kuka a mujami'ar Pentecostal dake sansanin 'yan gudun Bidi Bidi na arewacin Uganda

2
Wani mutune yana ratsawa ta cikin ruwa a kasar India

3
Wani matashi a cikin wani kwale-kwale yana kwasar sharar da za a iya sarrafa ta a birnin Jakarta na Indonesia

4
Uwargida Kate ta Cambridge (Hagu) tana murmushi yayin da take tafiya tare da Yarima William da Yarima Edward a lokacin gasar tseren dawakai a Ascot Ingila