Kotun soja a Sudan ta Kudu tana ci gaba da shari’ar sojoji 13 da ake tuhuma da yin fyade ma ma’aikatan agaji ‘yan kasashen waje da kuma kashe wata ‘yar jarida ‘yar kasar lokacin fada a Juba a watan Yulin bara
Domin karrama ranar yin Allah waddai da shaye-shayen miyagun kwayoyi a Najeriya Hukumar NDLEA ta gudanar da babban taron masu ruwa da tsaki domin jayo hankalin jam'a kan illar shaye-shayen miyagun kwayoyi dake halaka matasan kasar da yawa.
Jamus: Mutane Talatin da daya ne suka jikata, jami’an ‘yan sanda na kyautata zaton kusan wasu 18 sun rasa rayukansu yayin da wata motar Bus da yi karo da wata babbar mota a kan yanyar Bavarian kuma dukkan su suka kama da wuta.
Habasha: Shugabanin kasashen Afirka sun hadu a taron kungiyar hadin kan kasashen Afirka na 29, domin tattaunawa akan matsaloloin da suka addabi nahiyar
A kasar Najeriya kuma jami'ar Maiduguri ta haka wani rami kewayen jami'ar domin magance hare haren yan ta'addan Boko Haram.
A kasar Venezuela jami'an kasar na ci gaba da farautar wani da ake zargi da jefa gurneti kan kotun koli dake Birnin Caracas.
Iraqi: Sojoji sun ce sun sake kwato Muhimmin Masallacin nan na Al-nuri, wanda aka lalata a birnin Mosul, inda shugaban kungiyar ISIS ya yi shelar kafa daularsa, shekaru uku da suka gabata.
Rwanda: A karon farko za a gudanar da taron Hukumar Lafiya ta Duniya a Kigali, don nazarin kalubale da kuma damar da ake da ita wajen inganta kiwon laifya anahiyar Afirka.
A kasar Libya kuma yan ci rani su 25 daga kasar Kamaru, Sudan, Mali da kuma Senegal ne suka rasa rayukansu a teku a lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa Turai, inda aka gano gawarwakinsu a bakin tekun birnin Tripoli a ranar Talata.
A kasar Venezuela trauma na ci gaba da karuwa, bayan da wani jirig mai saukar ungulu ya kai wa kotun koli da wani ofishin gwamantin kasar hari, abinda shugaba Maduro ya kwatanta a matsayin harin ta’addanci.
Columbia: A kalla mutane shida sun mutu wasu 31 kuma sun bace bayan da wani kwale-kwale dauke da masu yawon bude ido 170 ya kife a tafkin El Penol.
Nigeria: ‘Yan sanda sun tabbatar cewa mutane 9 ne suka halaka wasu 13 kuma suka jikkata a wasu hare-haren da ‘yan kunar bakin wake suka kai a Maiduguri.
A babban birnin Washington DC, mun yi tattaki zuwa masallacin Turkawa mai suna Diyanat Center of America inda musulmi daga sassa daban-daban na yankin birnin Washington suka halarta, domin gudanar da sallar idi a wannan babban masallacin tare da sada zumunci da sauran ‘yan uwa musulmi.
A can kuma kasar Iran duban mutane ne suka fito suna zangazanga akantittuna Mashdad inda ake bikin ranar Jerusalem,don nuna goyon baya ga Palestinawa.
Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres yace wajibi ne akan shugabanin Sudan Ta Kudu da su kawo karshen yakin basasa da yayi sanadiyar kashe duban dubattun mutane da sa waso miliyoyin da dama su rasa muhallinsu na zama. .
Afghanistan: A kalla mutane 20 suka mutu, wasu 50 kuma suka jikkata bayan tashin bam da aka dana a mota a wajen wani banki a lardin Helmand.
Kwamitin Sulhun MDD ya goyi bayan kafa rundunar yaki da tsageru tare da dakile shigowa da makamai, miyagun kwayoyi da safarar mutane don magance ta’addanci a yankin sahel
Domin Kari