Alhamisar nan aka gudanar da wani taro na kasashen duniya a ma'aikatar harkokin wajen Amurka a kan yadda za atinkari matsalolin da kungiyar Daesh ko ISIS da saurai kungiyoyin ta'addanci suke haifarwa a sassan duniya dabam dabam.
Shugaban kasar Ruwanda Paul Kagame, ya gana da shugaban kasar Isra’ila Reuven Rivlin, da kuma Firayin minista Benjamin Netanyahu, a Birnin Kudis, ya kuma bayyana cewa zai karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu.
Niger: An nada Abdoulrazak Issoufou Alfaga, wanda ya lashe kambin wasannin Taekwondo na duniya, a matsayin Jakadan lumana na Hukumar UNICEF a ranar Jumma'a.
Za a horas da yan kungiyar boko haram din dasuka mika wuya,domin su koma yin rayuwa kamar yadda suke a da
A kasar Jamus ne aka gudanar da babban taron G20, mai masaukin, shugaba Angela Merkel tace ba tabbas na ko idan shugabannin dake halartar taron zasu iya samo hanyar magance matsalolin dake da alaka da sauyin yanayi da kasuwanci.
A birnin Paris na kasar Faransa kuma yan sanda ne suka kauda yan gudun hijira su 2500, 'yan kasashen Sudan, Eritrea da kuma wasu kasashe dake zaune a cikin wahala a arewacin birnin.
Rundunar sojin Najeriya ta yi tunawa da dakarun kasar a Maiduguri dake jihar Bornon, inda sojojin suka kai wa 'yan gudun hijira dake sansanin Bakassi taimakon magunguna.
Shugaban kasar Amurka ya gana da takawaransa na kasar Poland Andrzej Duda a birnin Warsaw, inda kuma Trump din ya gabatarda wani muhimmin jawabi.
Wani kanfani a kasar Kenya na kokarin taimkawa yanayi da inganta tsabta ta hanyar amfani da kashin bil adama da kuma tarkashe kura wajen kera bulon gine gine da mutane ke anfani da shi wajen girki.
A can kuma kasar China akalla mutane 5 ne suka mutu kana wasu 89 ne suka jikkata bayan fashewar wani bututun man fetur a arewacin kasar, wanda ya zama hadari na biyu a cikin wannan mako da gidan yada labaran kasar ya bayana.
Domin Kari